Da Gaske Wasu Sojoji Sun Yi Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu a Abuja? Gaskiya Ta Bayyana

Da Gaske Wasu Sojoji Sun Yi Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu a Abuja? Gaskiya Ta Bayyana

  • Rahotannin sun yi ta yawo cewar akwai yiwuwar yunkurin juyin mulki a fadar shugaban kasar Najeriya a daren jiya Lahadi
  • Rundunar ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa an ankarar da wasu daga masu tsaron shugaban kasar kan yunkurin da ake yadawa
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu jaridu sun wallafa cewa akwai alamun hakan yayin da aka ankarar da masu tsaron fadar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Rundunar sojin Najeriya ta yi martani kan zargin cewa akwai shirin juyin mulki a fadar shugaban kasar.

Rundunar ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa an ankarar da wasu daga masu tsaron shugaban kasar kan yunkurin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori uku na ba shi shawara kan tattalin arziki

Rundunar soji ta yi martani kan rade-radin yunkurin juyin mulki a fadar shugaban kasa
Rundunar soji ta karyata yunkurin juyin mulki a Najeriya. Hoto: Kola Sulaimon.
Asali: Getty Images

Menene ake yadawa kan juyin mulkin?

Hakan ya biyo rahotannin da wasu jaridu suka buga cewa an samu bayanan sirri kan shirin wasu na kifar da gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sahara Reporters na daya daga cikin wadanda suka wallafa labarin a daren jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu.

Rahoton nasu ya ce an gudanar da ganawar gaggawa tare da kwamandan masu tsaron fadar, Kanal Adebisi Onasanya da Shugaba Tinubu da shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila.

Martanin rundunar da fadar shugaban kasa kan lamarin

A martaninta, rundunar ta karyata wani abu da ke da alaka da hakan a shafinta na X kan wannan lamari inda ta ce labarin kanzon kurege ne.

Har ila yau, fadar shugaban kasar ta yi martani ita ma kan wannan labarin a shafinta na X a daren jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

Sanarwar ta ce:

"Ya zama dole kafafen sadarwa su matsa wurin tabbatar da kaucewa yada labaran karya, wannan labarin kanzon kurege ne."

Kabilar Ibo ta bukaci Gowon ya nemi afuwa

A wani labarin, Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta kabilar Ibo ta bukaci tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon a nemi afuwarsu.

Kungiyar ta ce Gowon ya tayar musu da ciwon da ya dade a zuciyarsu yayin ziyararsa ga Shugaba Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kalamai da tsohon shugaban kasar ya yi da ya shafi yakin Biafra da aka yi lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel