Yayin Da ’Yan Najeriya Ke Fatan Juyin Mulki, Sojoji Sun Tura Sako Ga ’Yan Kasar Kan Muhimmin Abu 1

Yayin Da ’Yan Najeriya Ke Fatan Juyin Mulki, Sojoji Sun Tura Sako Ga ’Yan Kasar Kan Muhimmin Abu 1

  • Rundunar tsaron Najeriya ta yi magana kan ‘yan kasar da ke yawan tsine mata kan halin kunci da mutanen kasar ke fama da shi
  • Hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ya roki ‘yan kasar da su bar tsine mata don hakan babu abin da zai kara musu
  • Janar din ya bayyana haka a jiya Talata 27 ga watan Faburairu inda ya ce tsinewa kasar babu abin da zai kara wa mai zagin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya roki ‘yan kasar da su bar tsine mata kan halin da ake ciki.

Musa ya bayyana haka a jiya Talata 27 ga watan Faburairu ida ya ce tsinewa kasar babu abin da zai kara wa mai tsinuwar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Sojin Najeriya ta tura sako mai muhimmanci ga 'yan kasar
Sojoji sun gargadi masu tsinewa Najeriya kan halin da ake ciki. Hoto: Gen. Christopher Musa.
Asali: Getty Images

Wane gargadi hafsan tsaron ya yi?

Ya ce dukkan wadanda ke zagi ko kushe kasar ko fatan sharri babu abin da zai kara musu kuma ba yana nufin za su ci gaba fiye da yadda suke ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Christopher Musa ya bayyana haka yayin wani taro a cibiyar rundunar da ke birnin Abuja inda ya ce dole ‘yan kasar su rike da hannu bibbiyu.

Ya ce rundunar ta himmatu wurin yin amfani da hanyoyi daban-daban don tabbatar da dakile matsalolin tsaro da ke damun kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan Najeriya ke neman sojin kasar ta aiwatar da juyin mulki kamar wasu kasashen Nahiyar Afirka.

Martanin rundunar kan masu fatan juyin mulki

Rundunar a martaninta kan kiran juyin mulkin ta gargadi masu kiran inda ta yi musu barazanar daukar mataki, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya ce sun batawa yan Najeriya lokaci, ya fadi tsarin mulkin da ya dace da kasar

Janar Musa shi ya bayyana haka inda ya ce duk masu kiran a yi juyin mulkin ba su da kishin kasa ko kadan a zuciyarsu.

Musa ya kara da cewa da zarar sun kama duk wani mai fatan haka a kasar zai fuskanci hukunci daga rundunar.

Sojin Najeriya sun musanta yunkurin juyin mulki

Kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi martani kan jita-jitar yunkurin juyin mulki a kasar da wasu jaridu suka yada.

Rundunar ta ce kwata-kwata babu wannar magana a kasar inda suka ce za su ci gaba da kare martabar dimukradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel