Ana Cikin Tsadar Rayuwa, Gwamnan PDP Zai Ɗauki Sabbin Malamai 5,000 da Ɗaruruwan Ma'aikata

Ana Cikin Tsadar Rayuwa, Gwamnan PDP Zai Ɗauki Sabbin Malamai 5,000 da Ɗaruruwan Ma'aikata

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya amince da ɗaukar sabbin malamai 5,000 da kuma ma'aikatan ilimi 250 a jihar
  • Sakataren watsa labaran gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce tuni gwamnati ta umarci ma'aikatar ilimi ta fara bin matakan da ya dace
  • Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin Adeleke ta amince da fitar da N1.3bn domin gyara aikin ruwan sha mai tsafta a ƙaramar hukumar Ifedayo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta amince da daukar sabbin malamai 5,000 da ma'aikatan ilimi 250.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin za ta ɗauki malamai da sabbin ma'aikatan ne domin cike gibin da ke akwai a harkokin koyarwa na jihar.

Kara karanta wannan

Kiwon Lafiya: Gwamnan APC ya amince da abu 1, zai ɗauki sabbin ma'aikata sama da 1,000

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun.
Gwamna Adeleke Zai Ɗauki Malamai 5,000 da Daruruwan Ma'aikata a Jihar Osun Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labaran gwamna, Olawale Rasheed, ranar Laraba a Osogbo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan, Gwamna Adeleke ya ce ya amince da ɗaukar sabbin malaman ne bayan kammala nazari da tantance buƙatun da ke akwai wanda gwamnatinsa ta yi a 2023.

Yaushe za a fara ɗaukar malamai a Osun?

Mista Rasheed ya kara da bayanin cewa an cimma wannan matsaya ne a wurin taron majalisar zartarwa ta jihar (SEC) bisa jagorancin Gwamna Adeleke.

Bugu da ƙari, ya ce majalisar ta umarci ma'aikatar ilimi ta gaggauta bin duk matakan da ya dace na ɗaukar aiki domin zaƙulo kwararru kuma masu gogewa.

A cewarsa, samun kwararrun malamai zai inganta harkar koyo da koyarwa a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, rahoton Tribune Online.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tono tushen matsalar ƴan bindiga a Arewa, ya jero hanyoyin magance su

Baya ga ɗaukar sabbin malamai, majalisar zartarwan Osun ta kuma amince da fitar zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 1.3 domin gyara ayyukan samar da ruwa.

Kakakin gwamnan ya ce kuɗin da aka fitar, za a yi amfani da su ne wajen gyara ayyukan samar da ruwan sha mai tsafta na Ora Igbomina a ƙaramar hukumar Ifedayo.

An fara duba kudin gyara dokokin zaɓe 2022

A wani rahoton kuma Kudirin sake garambawul a kundin dokokin zaben Najeriya 2022 ya tsallaka zuwa karatu na biyu a majalisar wakilan tarayya.

Majalisar ta amince da kudirin a zaman ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024 bayan ɗan majalisa daga jihar Delta ya gabatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel