Fitaccen Basarake a Arewa Ya Magantu Kan Halin Kunci, Ya Tura Sako Ga ’Yan Kasuwa Kan Tsadar Kaya

Fitaccen Basarake a Arewa Ya Magantu Kan Halin Kunci, Ya Tura Sako Ga ’Yan Kasuwa Kan Tsadar Kaya

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, Sarkin Gwandu ya shawarci ‘yan kasuwa kan jin tsoron Allah a harkokinsu
  • Mai Martaba, Alhaji Ilyasu Bashar ya bayyana haka ne a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu yayin ziyarar ‘yan kasauwar a fadarsa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kukan tsadar kayayyaki a kasar musamman na abinci tun bayan cire tallafin mai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi – Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammad Ilyasu Bashar ya shawarci ‘yn kasuwa kan jin tsoron Allah a harkokinsu.

Basaraken ya bayyana haka a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu a jihar Kebbi yayin da ‘yan kasuwa suka kai masa ziyara a fadarsa.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Babban basarake a Arewa ya shawarci 'yan kasuwa kan tsadar abinci
Sarkin Gwandu ya hori 'yan kasuwa su ji tsoron Allah a kasuwancinsu. Hoto: Alhaji Muhammad Ilyasu Bashar.
Asali: Facebook

Menene Sarkin ya ce kan 'yan kasuwa?

Yayin tattaunawa da ‘yan kasuwar, Mai Martaban ya shawarce su da su rinka siyar da kayansu kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kukan tsadar kayayyaki a kasar musamman na abinci tun bayan cire tallafin mai, cewar Daily Trust.

Ya ce bai kamata a ci gaba da zargin gwamnati ba kan wannan matsalar kowa akwai gudunmawar da ya bayar.

Wace shawara ya bai wa 'yan kasuwar?

A cewarsa:

“Dukkanmu abin zargi ne, ya kamata mu bar zargin gwamnati kowa ya zauna ya gani wace gudunmawa zai bayar don dakile matsalar.”

Ya ce madadin zargin gwamnati kan halin da aka shiga, ya kamata ‘yan kasuwa su zama masu adalci yayin siyar da kayayyakinsu, BNN News ta tattaro.

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwar da suka yi zama a fadarsa da su wayar wa sauran ‘yan kasuwar kai idan sun koma kan sakon da ya bayar.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

Mai sarautar ya ce dole kowa ya gyara halinsa tare da neman hanyar ba da gudunmawa da za ta kawo karshen wannan tsadar rayuwa da ake ciki.

Tinubu zai fara biyan matasa

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin biyan matasa musamman marasa aikin yi a Najeriya saboda halin matsi.

Shugaban ya ce matakin ya zama dole don dakile halin kunci da matasan ke ciki yayin da ake fama da tsadar rayuwa a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel