Malamin Addini Ya Fada ma Tinubu Abu 1 Da Ya Kamata Ayi da Mabuyar Boko Haram

Malamin Addini Ya Fada ma Tinubu Abu 1 Da Ya Kamata Ayi da Mabuyar Boko Haram

  • Fitaccen malamin addini, Primate Elijah Ayodele, ya ba gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan hanyar magance matsalar tsaro da karancin abinci
  • Malamin addinin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da mabuyar 'yan ta'addan Boko Haram su zama gonaki
  • Ya kuma yi kira ga tsohon 'dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi da ya hakura da takara a 2027 don ba shi ne zabin Allah ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Lagos - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da dazuzzukan da 'yan Boko Haram ke amfani da su a matsayin mabuyarsu su zama gonaki.

A cewar wata sanarwa da aka saki a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, Ayodele ya bayar da shawarar ne a ranar 18 ga watan Fabrairu, yayin bikin cikar cocin shekaru 30 a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

Primate Ayodele ya nemi a mayar da mabuyar Boko Haram gonaki
Malamin Addini Ya Fada ma Tinubu Abu 1 Da Ya Kamata Ayi da Mabuyar Boko Haram Hoto: Primate Elijah Ayodele/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Abin da mayar da mabuyar Boko Haram gonaki ke nufi, malamin addini

Malamin addinin ya ce mayar da mabuyar Boko Haram gonaki zai magance matsalar rashin tsaro da na karancin abinci, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce:

"Na shawarci gwamnatin tarayya da ta mayar da duk dazuzzukan da Boko Haram ke amfani da su a matsayin mabuyarsu su zama gonaki.
"Wannan matakin zai samar da karin amfanin gona da za a sayar a kan farashi mai rahusa, kuma shakka babu, ya kamata a haskaka abubuwan da ba a so, tare da nuna bukatar gwamnati ta karfafa tsarin tsaro a kasar."

Idan Obi ya zama shugaban kasa wahala za ta karu, Ayodele

Ayodele ya bukaci 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, a zaben 2023, da kada ya yi takarar shugaban kasa a 2027 saboda ba shi Allah ya zaba ba.

Kara karanta wannan

An tanadi buhuna 985,044 za a rabawa talakawa abinci Inji Fadar shugaban kasa

Jaridar Punch ta kuma nakalto yana cewa:

“Najeriya na fuskantar matsi a halin yanzu. Zamowar Peter Obi a matsayin shugaban kasa yana nufin karin wahalhalu zuwa mataki na hudu."

Abin da ya kamata gwamnati ta yi don kawo ci gaba, babban fasto

Ya roki gwamnatin tarayya da ta guji bai wa hukumomin gwamnati kudaden tallafi, yana mai cewa “Ba zai kai wajen talaka ba.”

A maimakon haka, ya ce ya kamata gwamnati ta taimaka wa masana’antun cikin gida wajen rage farashin dala da kuma inganta rayuwar jama’a.

Malamin ya kuma yi kira ga jama’a akan su rungumi soyayya domin dakile tashin hankali a cikin al'umma.

"Idan har Gwamnatin Tarayya za ta iya bin shawarwarina ta hanyar amfani da albarkatun kasa da ma’adinai, matsalar tserewa daga kasar zai zama tarihi," inji malamin.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani ‘dan Najeriya don jin ra’ayinsa game da shawarar da malamin addinin ya bayar na mayar da mabuyar Boko Haram ta zama gonaki.

Kara karanta wannan

Dakarun noma: Gwamnati ta dauki mataki 1 na tsare manoma daga farmakin 'yan bindiga

Malam Abdullahi wanda ke bibiyar al’amuran da ke faruwa a kasar ya ce:

"Wannan shawara da malamin ya bayar abu ne da ya kamata a kalle shi ta fuska biyu. Da farko dai shawara ce mai kyau idan har aka iya cimma nasarar yin noma a dajin da ‘yan ta’addan ke ta’asarsu.
“Amma tambaya a nan su wanene za su yi noman? A halin da ake ciki kuna ganin akwai wani manomi ko mutum da zai yarda ya je wadannan wuri da rashin tsaro da ake fama da shi a kasar? Bana tunanin akwai wanda zai yi wannan kasadar.
"Saboda basu da tabbacin samun isasshen kariya daga bangaren tsaro. Ku tuna fa nan aka bi manoma masu yawan gaske aka kashe a gonakinsu ba tare da an dau wani kwakkwaran mataki ba domin dai an yi hakan ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba.”

Ya ci gaba da yin bayani:

Kara karanta wannan

Gwamnati ta dakatar da fitar da iskar gas din girki zuwa kasashen waje, ta fadi dalili

“Abu na biyu idan aka ci nasarar yin nomar har aka girbe, wani tabbaci ake da shi na cewar amfanin gonan da aka samu zai isa ga talaka?
“Muna fa ji a nan tun kwanaki aka ce Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umurnin fito da hatsi daga rumbun ajiyar gwamnati don a rabawa talakawa amma har yau babu amo babu labari.
“Kawai dai mafita it ace gwamnati ta san abin da take ciki sannan ta nemi hanyoyin da za ta karfafa tsaron rayuka da abinci saboda bana tunanin akwai abin da ya fi karfin gwamnati idan har za ta bi ta hanyoyin da suka dace.
“Game da shawarwarin wannan malamin addinin kuma a nawa ra’ayin ina ganin ba wani tasiri sosai zai yi ba a yadda abubuwa suke ciki yanzu a kasar nan.”

Malamin addini ya magantu kan tabarbarewar naira

A wani labarin kuma, mun ji cewa fasto Ayodele, ya gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu kan halin da tattalin arziki ke ciki a yanzu

Malamin addinin ya ce Najeriya za ta fuskanci durkushewar tattalin arziki idan har ba a dauki matakan da suka cewa cikin gaggawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel