Sarkin Kano Ya Tuna da Talakawa, Ya Ba Remi Tinubu Sakonni 3 Ta Ba Shugaba Tinubu

Sarkin Kano Ya Tuna da Talakawa, Ya Ba Remi Tinubu Sakonni 3 Ta Ba Shugaba Tinubu

  • Remi Tinubu uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta kai ziyara a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero
  • A yayin ziyarar mai martaba Sarkin na Kano ya miƙa saƙonni uku da yake son Remi ta isar da su zuwa ga Shugaba Tinubu
  • Alhaji Aminu Ado Bayero ya gaya mata cewa ta isar da saƙon cewa talakawa na cikin wahala saboda yadda rayuwa ta yi tsada a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ƙarbi baƙuncin uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu a fadarsa da ke birnin Kano.

Sarkin na Kano a yayin ziyarar da uwargidan Tinubu ta kai masa, ya miƙa mata saƙonni waɗanda za ta ba shugaban ƙasan idan ta koma, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu: An tsaurara tsaro a Kano kan abu 1 tak

Sarkin Kano ya ba Remi Tinubu sakonni
Sarkin Kano ya bukaci Remi Tinubu ta sanar da Tinubu halin da talakawa ke ciki Hoto: Adeyanju Deji
Asali: Facebook

Mai martaba Sarkin na Kano ya gaya uwargidan shugaban ƙasan cewa mutanen Najeriya na cikin halin ƙunci, saboda haka ya kamata ya yi abin da ya dace don shawo kan matsalar, rahoton Aminiya ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma buƙaci Tinubu da ya sake duba lamarin ɗauke hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN), da wasu sasan babban bankin Najeriya (CBN) daga birnin Abuja zuwa Legas.

Waɗanne saƙonni Sarkin Kano ya ba Remi Tinubu?

Saƙonni Sarkin na Kano zuwa ga Shugaba Tinubu sun haɗa da:

1. Al’amura sun kai inda suka kai a ƙasa, kayan abinci sun yi tsada, jama'a na cikin halin wahala.

2. Ya kamata a magance matsalar tsaro wacce ta yi wa jama'a katutu.

3. Akwai buƙatar sake tunani kan shirin ɗauke ukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) da wasu sassan babban bankin Najeria (CBN) daga Abuja zuwa Legas.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya samo mafita ga 'yan Najeriya

Sarkin Kano ya jaddada buƙatar gwamnatin Tinubu ta kawo wa talakawa agajin gaggawa domin su samu sauƙin wahalhalu da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan.

Ziyarar Remi Tinubu Zuwa Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tsaurara matakan tsaro a birnin Kano, a yayin ziyarar da uwargidan shugaban ƙasa za ta kai birnin.

Remi Tinubu za ta ziyarci birnin na Kano ne domin ƙaddamar da ginin tsangayar karatun lauyoyi da aka sanya sunanta, a jami'ar Maryam Abacha da ke Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel