Matakin Tinubu 1 Ya Jefa Najeriya a Wahala Inji Sakataren Gwamnatin Buhari

Matakin Tinubu 1 Ya Jefa Najeriya a Wahala Inji Sakataren Gwamnatin Buhari

  • Babachir David Lawal ya yi tir da yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tayi gaggawan yin waje da tsarin biyan tallafin fetur
  • ‘Dan siyasar ya ce sabon shugaban kasar ya dauki mataki ne tun ranar farko ba tare da ya tuntubi wadanda suka kamata ba
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyan yana tare da Bola Tinubu kafin tikitin musulmi da musulmi ya rabu su da zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Babachir David Lawal wanda ya yi sakataren gwamnatin tarayya a Najeriya ya soki yadda aka soke tsarin tallafin man fetur.

A wata zantawa da The Cable tayi da shi, Babachir David Lawal ya zargi Bola Ahmed Tinubu da gadara wajen cire tallafi a kan fetur.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur a Najeriya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya jawo wahalar tsadar fetur

‘Dan siyasar yake cewa garaje da sabon shugaban Najeriyan ya yi ranar da aka rantsar da shi ya jefa Najeriya a cikin kuncin rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon jagoran na APC mai mulki ya zargi Bola Ahmed Tinubu da nuna rashin imani da girman kai tun wajen dauko abokin takaransa.

Babachir yana ganin bai dace a matsayinsa na musulmi, Tinubu ya dauko musulmi ba, bayan nan kuma sai ya jawo fetur ya kara tsada.

Zancen Babachir David Lawal

"Ra’ayina shi ne girman kai ya tunzura aka cire tallafin fetur. An rantsar da kai kuma kana son nuna kai ne a kan karagar mulki yanzu,
Za ka iya danne kowa, sai kurum ka sanar da cire tallafi ba tare da tuntubar kowa ba."

- Babachir David Lawal

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi zancen mayar da tallafi da soke karya naira saboda shiga kuncin rayuwa

Tinubu bai yi koyi da magabata ba

An rahoto Babachir yana cewa ya kamata shugaba Tinubu ya tuntubi mukarrabasa da masu ruwa da tsaki kafin ya dauki mataki.

Kafin Olusegun Obasanjo ya cire tallafi sai da ya kirkiro SURE-P, yake cewa Janar Sani Abacha ya kafa PTF da ya tashi kudin fetur.

Duka tsadar rayuwa da wahalar da ake ciki a yau, Babachir ya ce Tinubu ya jawowa kan sa.

Tinubu ya nada mukamai a gwamnati

Ana da labari Mai girma Bola Tinubu ya nada Darektoci da Kwamishinonin da za su rika hukumomin NCC da NIGCOMSAT a Najeriya.

Ibrahim Adepoju Adeyanju wanda mataimakin Farfesa ne a jami’ar Oye Ekiti ne zai zama shugaban kamfanin Galaxy Back Bone Ltd.

Opeyemi Dele-Ajayi wanda yake aiki da kamfanin Meta masu Facebook ya samu mukami a gwamnatin tarayya a nadin mukaman da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel