An Debi Garabasa: Jama'a Sun Mamaye ‘Dan Kasuwa Bayan da Ya Samar da Shinkafa Mai Sauki, Buhu N58k

An Debi Garabasa: Jama'a Sun Mamaye ‘Dan Kasuwa Bayan da Ya Samar da Shinkafa Mai Sauki, Buhu N58k

  • Wani ‘dan Najeriya na siyar da buhun shinkafa kan N58,000, kuma mutane da dama sun nuna ra’ayinsu na son siya a wajensa
  • Matashin, Haidar Abdullahi Gaduwama, ya yi wata wallafa a shafin X, yana mai tallata shinkafarsa buhuhunan 50kg
  • Haidar ya sanar da jaridar Legit.ng cewa shi da kansa ya noma shinkafar tare da sarrafawa, wanda shine dalilin da yasa farashinsa ya bambanta da na saura

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani 'dan kasuwa ya bayyana cewa yana siyar da kowani buhun shinkafa kan N58,000, kuma cewa yana iya kai wa mutum duk inda yake a fadin Najeriya.

Haidar Abdullahi Gaduwama ya tallata haajarsa a dandalin X, kuma akwai mutane da dama da suka bibiyi shafinsa, suna masu nuna ra’ayinsu na son siya a wajen sa.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Matashi ya samar da shinkafa mai sauki
An Debi Garabasa: Jama'a Sun Mamaye ‘Dan Kasuwa Bayan da Ya Samar da Shinkafa Mai Sauki, Buhu N58k Hoto: Haidar Abdullahi Gaduwama.
Asali: UGC

Farashin shinkafa da sauran kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi a Najeriya yayin da ake ci gaba da fama da tsadar rayuwa a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya rubuta a shafin X:

“Ina siyar da wannan buhun 50kg na shinkafa ‘yar Najeriya, zara-zara kuma mara dutse kan 58k kacal. Aiko mani da sako idan kana ra’ayi, zo mu yi kasuwanci.”

Dalilin da yasa shinkafar ke da sauki, Haidar

Jaridar Legit ta zanta da shi, kuma ya ce shi da kansa ya yi noman wasu daga cikin shinkafar a Hadejia, jihar Jigawa.

Kalamansa:

“Da farko, muna noma shinkafarmu a Hadejia, jihar Jigawa. Amma kuma muna siyar shinkafa shanshara daga wajen manoma a fadin jihar, sai mu sarrafa sannan mu zuba ta a buhu don siyarwa.
“Ina ganin shinkafata tana da sauki saboda ni ke nomawa, na sarrafa sannan na hada ta da kaina ba tare da wani ya shigo lamarin ba. Kamar dai siya kai tsaye don rage tsada mara amfani.”

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

Haidar, wanda ya ce ya fara sana’ar shinkafa a 2021, ya bayyana cewa na shi akwai arha saboda sauran mutane suna siyarwa ne tsakanin N65,000 zuwa N68,000.

Ya ce shinkafar gida Najeriya na da inganci domin dai ana sarrafata ne kamar yadda ake yin ‘yar waje.

Jama'a sun yi martani

@Abdul_x2 ya tambaya:

"Nawa kudin kawowa Ilorin?"

@Bin_Ussein ya tambaya:

"Nawa ake kawo kowani buhu zuwa jihar Osun?"

@emmaculatee1 ya yi martani:

"Don Allah aiko mani da sako, ina da wani da ke bukatar shinkafar Najeriya fiye da buhuhuna 150."

Sanata ya fadi hanyar mallakjar abinci cikin sauki

A wani labarin, mun ji cewa Muhammad Ali Ndume da wasu abokan aikinsa da ke majalisa sun kawo kudirin da ake sa rai zai taimaka a wajen rage yunwa.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce suna kokarin kirkiro da katin sayen abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel