Yunwa: Kwanaki 15 da Alkawarin Tinubu, Har Yanzu Ba a Rabawa Talaka Kayan Abinci ba

Yunwa: Kwanaki 15 da Alkawarin Tinubu, Har Yanzu Ba a Rabawa Talaka Kayan Abinci ba

  • Tun a farkon watan nan aka ce Bola Ahmed Tinubu ya yi umarni a bude rumbunan gwamnatin tarayya a fito da abinci
  • Makonni bayan wannan alkawari da shugaban kasar ya yi, ba a ga buhunan hatsin balle a soma rabawa masu bukatar ba
  • Hukumar NEMA da ministan aikin gona ya ce za a damkawa abincin su rabawa mutane suna jiran gwamnati ta cika alkawarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Makonni biyu da suka gabata aka rahoto cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi umarni a fito da buhunan abinci domin rabawa mutane.

Wani rahoton Daily Trust ya tunawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu cewa yanzu makonni biyu da yin wannan alkawari amma ba a cika ba.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Gwamnati za ta fara raba kyautan kudi ga talakawa miliyan 12, Minista

Abinci
Bola Tinubu ya yi alkawarin raba abinci Hoto: @Dolusegun/Getty Images (Hoton bai da alaka da labarin)
Asali: UGC

Gwamnatin tarayya za tayi rabon hatsi

A wancan lokaci, gwamnatin tarayya ta ce za a fito da hatsin ne daga rumbunan Najeriya domin raba su ga marasa hali da ke cikin kunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya zama dole bayan ganin yadda farashin abinci suka tashi a kasuwanni. Gwamnati ta dage wajen ganin an samu sauki a kasar.

Minista ya ce NEMA za ta raba abincin

Tun ranar Laraba, 8 ga watan Fubrairu, 2023, Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya ce talakawa za su rabawa hatsin.

A yau kwanaki 15 kenan da Sanata Abubakar Kyari ya sha wannan alwashi, Legit ba ta da labarin wani talaka da aka ba kyautar abinci.

Gwamnati ta ba NEMA kayan abinci?

Hukumar NEMA da aka yi ikirari za a fitar da abincin ta hannunta ba ta fara aikin ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gama shirin raba buhuna miliyan 1.4 na kayan abinci a jihohi - Minista

Rahoton ya ce da aka bincika jihohi irinsu Kano, an fahimci cewa gwamnatin tarayya ko NEMA ba ta aiko da komai ba har zuwa jiya.

Babu ko mudun hatsin a ofisoshin NEMA da ke Ogun, Oyo, Neja, Bauchi, Yobe, Kogi haka zalika Benuwai, Nasarawa da kuma Kuros Riba.

Shugaban harkokin NEMA ta jihohin Neja da Kwara, Zainab Saidu ta shaidawa jaridar cewa ba a kawo masu buhunan hatsi ba tukun.

Haka lamarin yake a sauran jihohin kasar nan inda tuni mutane sun fara zanga-zanga.

Za a raba karin kayan abinci

A makon nan aka samu rahoto Ministan tattalin arziki ya bayyana shirin da ake yi domin karya farashin kayan abinci a kasuwannin kasar.

Wale Edun ya ce Bola Tinubu ya amince a fito da karin metric ton 60, 000 da za a rabawa talakawa, kari a kan alkawarin da aka yi da farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel