Jiga jigan Arewa na Neman Hadaka Domin Kawar da Ganduje Daga Shugabancin APC

Jiga jigan Arewa na Neman Hadaka Domin Kawar da Ganduje Daga Shugabancin APC

  • Tsagin APC na Arewa maso tsakiya ya gudanar da taro a jihar Kaduna domin yunkurin tsige Abdullahi Umar Ganduje
  • Shugaban tsagin Alhaji Saleh Mandung Zazzaga ya ce babu bukatar cigaba da shugabancin Ganduje a halin yanzu
  • Zazzaga ya bayyana matakai da suka dauka domin ganin Abdullahi Ganduje ya sauka daga kujerar cikin gaggawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tun bayan sanar da korar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da wasu suka yi a mazabarsa, ya cigaba da samun barazana.

ABdullahi Ganduje Shugaban APC
An fara sabon yunkurin kawar da Ganduje daga kujerar APC. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Kujerar Abdullahi Ganduje tana yawo a APC

Barazanar ta kai ga yin zanga-zanga da mika kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ya sauke Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kwanaki bayan samun mukami, tsohon Gwamna ya kare Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabuwar barazana ta kara fitowa Ganduje daga tsagin APC da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya, cewar jaridar Daily Trust.

Tsagin APC ya yi taro kan Ganduje

Tsagin APC da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya ya shirya taron masu ruwa da tsaki ranar Lahadi kan raba Ganduje da kujerar shugabancin jam'iyyar.

Cikin jawabin karshen taro da tsagin ya fitar ya yi kira ga uwar jam'iyyar a yanki a guji goyon bayan Ganduje.

Jawabin shugaban tsagin APC

Shuagaban tsagin APC na Arewa ta tsakiya Alhaji Saleh Mandung Zazzaga ya ce a yanzu kusan kowa ya juya wa Ganduje baya a APC, ciki har da mazabarsa.

Saboda haka ya ce a halin yanzu babu wata bukatar kasancewar Abdullahi Ganduje kan kujerar shugabancin jam'iyyar.

Kokarin da ake kan sauke Ganduje

Alhaji Saleh Mandung ya ce a halin yanzu sun fara tattaunawa da shugabannin APC a Arewa ta yamma domin ganin sun kori Ganduje.

Kara karanta wannan

Ganduje: Shirin tsige shugaban APC na ƙasa da maye gurbinsa ya gamu da cikas

Ya kara da cewa sun yi kira ga shugaba Tinubu kan dawo da shugabancin yankinsu kamar yadda tsarin jam'iyyar ya tanadar, rahoton Leadership.

A karshe ya ce ba za su zuba ido Ganduje ya cigaba da rike muƙamin da yake na yankinsu ba, za su cigaba da kori har sai sun ga bayansa.

Yan APC za su gana da Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jamiyyar APC na ƙasa zai samu manyan baki a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugabannin jam'iyyar na mazaɓun da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa za su ziyarci Ganduje domin nuna goyon bayansu a gare shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel