Wata Mahaifiya Ta Kashe Danta Mai Shekara 1 a Jihar Delta

Wata Mahaifiya Ta Kashe Danta Mai Shekara 1 a Jihar Delta

  • Wata mata 'yar shekara 24 mai suna Sophia Nkwor ta kashe dan cikinta ta hanyar jefa shi rijiya a jihar Delta
  • Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kama matar
  • Bayan gabatar da binciken 'yan sanda matar ta amsa laifin kisan tare da bayyana dalilan da suka sa ta kashe dan nata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Rahotannin da ke fitowa daga jihar Delta sun nuna cewa wata mata ta kashe danta mai shekara daya.

Nigerian Police
Wata mata ta kashe danta saboda damuwar duniya a jihar Delta. Hoto Nigerian Police Force
Asali: Facebook

A cewar matar 'yar shekara 24 mai suna Sophia Nkwor ta kashe yaron ne ta hanayar jefa shi cikin rijiya.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya bayan kama jarumin fina finai da zargin sace budurwa mai shekaru 14

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Araya da ke karamar hukumar Isoko a jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin rundunar 'yan sanda

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kama matar.

Ya kara da cewa tuni aka kai matar hedikwatar 'yan sanda tare da hada ta da masu laifuka irin nata, cewar jaridar Leadership

Yadda aka gano matar shi ne lokacin da sauran yara suka fita suna wasa sai suka ga gawar yaron a cikin rijiyar.

Daga nan ne rundunar 'yan sanda ta gaggauta kama mahaifiyar kuma ta amsa laifin bayan da aka binciketa.

Dalilin da ya sa ta kashe yaron

Ta kuma tabbatar da cewa ta jefa yaron ne cikin rijiya tun 26 ga watan Afrilu saboda ba za ta iya daukan dawainiyarsa ba.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Kano suka yi wawason 'yan daba sama da 3000 a shekara 1

Ta kara da cewa mahaifin yaron ya ce ya barranta da shi saboda haka dukkan dawainiyarsa tana kanta kuma ita ma bata da abin yi.

A cewarta, babu mai taimakonta wurin daukar dawainiyar kuma lokacin da ta aikata laifin ranta ya ɓaci ne.

Kotu ta kama dan Sin kan kisan kai

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun Kano ta yanke hukunci kan ɗan Sin da ake zargi da kisan Ummita bayan tsawon lokaci ana shari'a

Mai shari'a Sanusi Ado Ma’aji ya kama Mista Quandong Geng, ɗan kasar Sin da laifin kisan kai, bisa haka ya yanke masa hukuncin kisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel