Kaso 35%: Ba Mafi Karancin Albashi Gwamnati ta Kara ba, Cewar TUC

Kaso 35%: Ba Mafi Karancin Albashi Gwamnati ta Kara ba, Cewar TUC

  • Kungiyar 'yan kasuwa ta TUC ta yi karin bayani kan karin albashin da gwamnatin tarayya tace ta yi wa ma'aikata, inda tace ba mafi karanci ba ne
  • A cewar mataimakin shugaban kungiyar, Tommy Okon karin da gwamnatin ta yi cike gibin albashin wasu ma'aikata ne kawai ba mafi karancin albashi ba
  • Mataimakin shugaban ya ce har yanzu ana teburin tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja - Kungiyar kwadago ta 'yan Kasuwa (TUC) ta magantu kan karin 35% na albashin ma'aikata da gwamnatin tarayya tace ta yi a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Kwana 7: kungiyoyin kwadago sun bawa gwamnati wa'adin janye karin kudin wuta

TUC, ta bakin mataimakin shugabanta, Mista Tommy Okon ta ce karin ba shi ne mafi karancin albashi ba.

Tun bayan ayyana karin kungiyoyi su ka ce ba za su amince da shi a matsayin mafi karancin albashi ba
TUC ta ce karin wani gyara gwamnati ta yi kawai Hoto:Getty images
Asali: Getty Images

A rahoton da Vanguard News ta wallafa, ya ce gwamnati ta yi karin albashin ne domin cike gibin bambancin da ake da shi tsakanin ma'aikatan wasu ma'aikatun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnati ba ta shammace mu ba," TUC

Kungiyar 'yan kasuwa ta TUC ta ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta shammace su ta ayyana sabon mafi karancin albashi ba.

A cewar mataimakin shugaban kungiyar, Tommy Okon, har yanzu ana teburin tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Ya ce sabon karin da gwamnatin tarayya ta yi kari ne ga ma'aikatan gwamnatin tarayya, kamar yadda Newsnow Nigeria ta wallafa.

Mista Tommy Okon ya danganta karin da kokarin dawo da ma'aikatan dai-dai da takwarorinsu na wasu bangarorin da aka yi wa karin a baya.

Kara karanta wannan

1 ga watan Mayu: Gwamnati ta fadi ranar da sabon albashin ma'aikata zai fara aiki

A kalaman Mista Ikon;

“Wa su suna ganin kamar gwamnatin ta tsallake kungiyoyin kwadago sannan ta bayyana mafi karancin albashi ba tare da saninsu ba, amma fa karin ba mafi karancin albashi ba ne."

Gwamnati ta amince da karin albashi

Mun ruwaito maku a baya cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da karin albashi ga ma'aikatanta da kaso 25% zuwa kaso 35% a ranar ma'aikata.

Wadanda aka yi wa karin albashin kaso 25% da 35% su ne wadanda ke tsarin albashin bai daya na CONPSS, CONRAISS, CONPOSS, CONPASS, CONICCS da CONAFSS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel