Atiku Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Haddasa Tashin Dala da Rugujewar Tattali a Wata 8

Atiku Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Haddasa Tashin Dala da Rugujewar Tattali a Wata 8

  • Atiku Abubakar yana ganin babu wanda ya jefa kasar nan cikin kunci da matsalar lambar tattalin arziki irin Bola Ahmed Tinubu
  • Wazirin Adamawa ya ce manufofin sabuwar gwamnatin nan ba za su iya kawowa al’umma saukin rayuwar da ake tsammani ba
  • Atiku ya zargi Tinubu da jami’an gwamnatinsa da daukar mataki ba tare da an tuntubi masu ruwa da tsaki a Najeriya ba

Abuja - Atiku Abubakar wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya soki manufofin Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya yi doguwar magana a X a ranar Lahadi, ya zargi Bola Ahmed Tinubu da jefa tattali a matsala.

Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Atiku Abubakar ya soki Gwamnatin Bola Tinubu Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku ya soki tsarin gwamnatin Tinubu

Atiku Abubakar yana ganin kura-kuren gwamnatin Tinubu sun gurgunta tattalin arzikin Najeriya, ya ce ta jawo tashin da Dala ta ke yi.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa, Atiku wanda ya zo na biyu a zaben 2023 ya ce kyau a canza irin salon da ake dauka wajen magance halin da kasar ke ciki.

Jawabin Atiku Abubakar

"A zaman da aka yi na ranar Alhamis domin magance matsalolin kudin kasar waje da matsalar rushewar tattalin arziki da sauransu, Bola Tinubu ya sake nuna gwamnatinsa ba ta da wasu kwararan tsare-tsare domin shawo kan matsalolin hauhawan kudi da talauci da kasar ta k fuskanta."
"A maimakon haka sai ya fadawa kasar cewa a daina kauda hankalin masanan da ke bada shawarar yadda za a shawo kan matsalar kuma a ba su lokaci domin cigaba da bushasharsu da ta jefa kasar a matsala."

- Atiku Abubakar

Wazirin Adamawa ya ce ba za su yi shiru a rika wahalar da mutane da tsare-tsaren APC ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Kuskuren Tinubu a fannin tattalin arziki?

A matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, Atiku ya ce mafitar matsin lambar tattalin arzikin su na cikin takardar manufofin da ya gabatar.

Babban jagoran adawar ya yarda dole a daidaita farashin kudin waje, yana mai cewa dama ya san dole za a burma yanayin da aka shiga.

Duk da ya ce Najeriya ba ta da dalolin da za ta kare darajar Naira, Atiku ya ce an yi garajen daukar mataki ba tare da tuntubar masana ba.

Tinubu ba zai bude iyakoki ba

An ji labari Bola Tinubu ya ki daukar shawarar Kashim Shettima ta kayyade farashin abinci, ya ce a gida za a noma duk abin da ake bukata.

Gwamnatin tarayya ta yi jan-kunne a game da hadarin bude iyakoki domin a shigo da abinci, a ganinta wannan zai karya manoman kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel