Aiki na Kyau: Dalilin Shugaban kasa Tinubu Na Ware Abba, Ya Jinjina Masa Cikin Gwamnoni

Aiki na Kyau: Dalilin Shugaban kasa Tinubu Na Ware Abba, Ya Jinjina Masa Cikin Gwamnoni

  • Kwanakin baya Abba Kabir Yusuf ya koka game da yadda farashin shinkafa da kayan abinci suka tashi a Kano
  • A sakamakon haka gwamnan ya zauna da ‘yan kasuwa, ya dauki matakin karya masu boye kayayyakin abinci
  • Shugaban kasa Bola Tinubu yana lura da abubuwan da ke faruwa, ya yi kira ga gwamnoni su bi sahun Abba Gida Gida

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da gwamnonin jihohin kasar nan a fadar Aso Rock Villa a dalilin tsadar rayuwa.

A wajen wannan zama da aka yi, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matakan gaggawa da ya kamata gwamnatoci su dauka.

Bola Tinubu - Abba Kabir Yusuf
Bola Tinubu ya yabawa Abba Kabir Yusuf wajen taron Gwamnoni a Aso Rock Hoto; @Dolusegun16, @KyusufAbba
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya soki yadda ‘yan kasuwa su ke boye kayan abinci a irin wannan yanayi.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yabawa Abba Gida Gida

A dalilin haka ne ya yabawa gwamnan jihar Kano a game da matakin da ya dauka wajen ganin bayan wannan mummunar al’adar.

Jawabin bayan taro da Bayo Onanuga ya fitar ya nuna Bola Tinubu ya ba gwamnoni shawara suyi koyi da salon Abba Kabir Yusuf.

Gwamnatin tarayya ta lura da yadda hukumar sauraron korafi da yaki da rashin gaskiya ta jihar Kano ta ke hana boye abinci.

Tinubu ya haramta boye abinci

Tinubu ya umarci Sufetan ‘yan sanda, Mai bada shawara a kan tsaro da jami’an hukumar DSS su sa ido a kan masu boye kaya.

Kamar yadda aka samu labari, jami’an tsaro za su ga bayan masu neman cin kazamar riba da mutane a lokacin da ake yunwa.

Shawarar Tinubu ga Gwamnoni

Daga cikin shawarwarin da shugaban kasa ya ba gwamnoni shi ne a daina wasa da albashi da fansho sannan a kawo ayyukan yi.

Kara karanta wannan

"Sun rasa muryarsu karkashin Buhari": Shehu Sani ya magantu yayin da sarakunan Arewa ke sukar Tinubu

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda bai halarci taron da aka yi jiya ba ya fara biyan tsofaffin ma’aikata hakkinsu a Kano tun a bara.

Domin bunkasa harkar noma, gwamnan ya nemi taimakon gwamnatin Kanada saboda a ci moriyar dam da ake da su a jihar.

Masu boye abinci a Kano

Muhuyi Rimin Gado ya zauna da ‘yan kasuwan Kano, daga nan ya rika fasa dakunan aka ajiye abinci da nufin ganin farashin ya sauko.

Ana zargin wasu su na boye kaya a wannan kaka da nufin su fito da su idan sun yi tsada.

‘Yan kasuwa da yawa sun musanya zargi nan, su na cewa canjin farashin da ake samu daga kamfanoni ne, ba su suka jawo karin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel