Muhimman abubuwa game da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum

Muhimman abubuwa game da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum

An rantsar da Farfesa Bababgana Umara Zulum a matsayin zababben gwamnan jihar Borno a ranar 29 ga watan Mayun 2019. Ya gaji tsohon gwamnan jihar, wanda Sanata ne a halin yanzu, Kashin Shettima duk karkashin jam’iyyar APC.

Mutane sun bada shaidar Babagana kan yadda bai damu da wasu kyale-kyalen duniya ba duba da manyan mukaman da ya rike amma bai tara ba.

An haifa Farfesa Zulum a ranar 26 ga watan Agustan 1969 a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno. Yayi karatun firamare a mafa inda yayi na sakandire a Monguno daga 1975 zuwa 1985. Tun kuwa yana aji biyar na sakandare ne ya mayar da hankalin daukar nauyin karatunsa da kansa.

A haka ya shiga sana’ar tukin mota a 1984 inda ya dau shekaru 16 yana wannan aikin.

A 1986 ne Zulum ya samu gurbin karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ramat da ke Maiduguri domin karantar fasahar ban ruwa da noman rani. Domin samun karin kudin tallafawa karatunsa, Zulum ya fara sana’ar markade a ranakun Asabar da Lahadi.

Muhimman abubuwa game da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum
Muhimman abubuwa game da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kotun koli ta tafka kuskure a yanke hukuncin kwace kujerar gwamnan Bayelsa - Falana

Ya kammala karatunsa na difloma a 1988 inda ya fara aiki a ma’aikatar noma ta jihar Borno tsakanin 1988 zuwa 1989. Daga baya ya koma hukumar kananan hukumomi ta jihar Borno.

A 1994 ne ya samu gurbin karatu a jami’ar Maiduguri don kammala digirinsa na farko. Bayan nan ya koma jami’ar Najeriya da ke Ibadan inda yayi digirinsa na biyu kan fasahar noma.

Amma kuma kafin fara digiri na biyu, ya dau makonni uku domin yin sana’ar kabu-kabu da mota don samun kudin rijistar zangon karatun. Bayan kammalawarsa a 1998, Zulum ya koma jihar Borno a matakin babban injiniyan noma a jihar.

Ya koma jami’ar Maiduguri a matsayin malami inda a nan ya samu digiri na uku.

Ganin jajircewar Babagana da tarihin da ya kafa, Kashim Shettima ya nada Zulum a matsayin shugaban kwalejjin kimiyya ta Ramat. Ko a lokacin kuwa, Zulum ya ci gaba da karbar albashinsa a matsayin malamin makaranta ba shugaban jami’a ba.

Gwamnan Kashim ya ba shi kwamishinan lura da sake gina yankin da Boko Haram suka lalata kuma ya mayar da hankali.

Ko a lokacin da jam’iyyar APC ta bayyana Zulum a matsayin wanda zai tsaya takararta a 2019, ya riga ya yi suna a jihar bisa tarihin da ya kafa na jajircewa wajen aiki da rikon amana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng