Ana Kokarin Cire Tallafin Lantarki, Majalisa Ta Bukaci Saka Tallafi a Wuri Mai Muhimmanci Ga Musulmi

Ana Kokarin Cire Tallafin Lantarki, Majalisa Ta Bukaci Saka Tallafi a Wuri Mai Muhimmanci Ga Musulmi

  • Yayin da ake kokarin cire tallafi a wutar lantarki bayan na man fetur, bangaren aikin hajjin ka iya samu tallafi don rage tsadar kujerar
  • Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci saka tallafi a harkar jigilar maniyya aikin hajji saboda muhimmancinsa a addinin Musulunci
  • Dan Majalisar, Umar Shehu Ajilo shi ne ya gabatar da kudirin a yau Alhamis yayin zaman Majalisar a birnin Tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci saka tallafi a harkar jigilar maniyya aikin hajji saboda muhimmancinsa.

Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta saka tallafi a hajjin bana don bai wa maniyyata damar zuwa kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Kano: Fitaccen dan kasuwa, Dantata ya fadi tsarin mulki da ya fi dacewa da Najeriya, ya fadi dalili

An bukaci saka tallafi a bangaren aikin hajji a Najeriya
Majalisa Ta Bukaci Saka Tallafi a Bangaren Jigilar Maniyya Don Samun Sauki. Hoto: Abbas Tajudden, NAHCON.
Asali: Facebook

Mene bukatar Majalisar kan aikin hajji?

Dan Majalisar, Umar Shehu Ajilo shi ne ya gabatar da kudirin a yau Alhamis yayin zaman Majalisar a birnin Abuja, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajilo ya kuma kirayi kwamitin Majalisar da ke kula da hukumar NAHCON da ta tilasta hukumar mayar da kudaden yadda mutane za su iya biya.

Umar ya kuma bayyana muhimmancin aikin hajjin a matsayin wata ibada mai girma a rukunan Musulunci.

Dalilin bukatar saka tallafin

Ya koka kan yadda kan yadda aka saka kudaden aikin hajjin bana da tsada har naira miliyan biyar da ya ce ya yi yawa, cewar Premium Times.

Ya kara da cewa ganin yadda rayuwa ta yi tsada a yanzu ya kamata a duba bangaren aikin hajjin saboda mutane su samu damar kai ziyara dakin Allah.

Kara karanta wannan

Jerin Sanatoci 45 da aka zaba domin aikin kwaskwarimar kundin tsarin mulki a majalisa

Kudurin ya samu goyon bayan mafi yawan mambobin Majalisar bayan Shugabanta, Abba Tajudden ya ba da damar fadin ra’ayi.

Wannan na zuwa ne yayin da aka cire tallafin man fetur da kuma kokarin cire na wutar lantarki a kasar.

NAHCON ta sanar da rage kudin kujera

Kun ji cewa hukumar NAHCON ta sanar da rage farashin kujerar aikin hajjin bana na 2024.

Hukumar ta ce sun samu ragin ne daga hukumomin Saudiyya ta bangaren kudin tikiti da wurin zama da sauransu.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokawa kan tsadar farashin kujerun a bana yayin da ake cikin wani hali a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel