Ana Daf da Rufe Rijista a Yau, NAHCON Ta Koka Yayin da Ta Fadi Yawan Kujerun da Aka Cike a Najeriya

Ana Daf da Rufe Rijista a Yau, NAHCON Ta Koka Yayin da Ta Fadi Yawan Kujerun da Aka Cike a Najeriya

  • Duk da sanar da cewa an samu ragi a kujerun aikin hajjin bana, da alamu ba a iya cike gubin kujerun da hukumar ta tanadar ba
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkan jihohin Najeriya ba su iya cike ko da rabin yawan kujerun da aka ware musu ba
  • Hukumar ta ware kujeru dubu 75 ga jihohi 36 da kuma Abuja inda ta ware kujeru dubu 20 ga kamfanoni masu zaman kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Da alamu Najeriya ba za ta iya cike gurbin yawan kujeru da aka ba ta ba na aikin hajji a wannan shekara.

Mafi yawan maniyyatan a wannan shekara ba su iya biyan dukkan kudaden aikin hajjin ba yayin da wasu ko ajiya ba su fara ba.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Hukumar NAHCON ta koka kan rashin cike kujerun aikin hajji bana
An gagara cike rabin kujerun aikin hajjin bana da aka ware. Hoto: NAHCON.
Asali: Facebook

Wace matsala aka samu a bana?

Matsalar darajar naira ta ba da gudunmawa wurin tsadar kujerar wanda ta kai miliyan 4.9 madadin miliyan 4.5 da aka sanar a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar jin dadin alhazai ta NAHCON a ranar 3 ga watan Faburairu ta sanar da kudaden aikin hajjin bana.

Yayin da ko rabi na kujerun ba a cike ba, Hukumar ta ce matsalar ba iya Najeriya ba ne.

Ta ce kasashe kamar Pakistan da Bangladesh da sauran kasashe sun koka kan irin matsalar rashin cike kujerun.

A cikin sanarwar ta ce maniyyata daga Kudancin Najeriya za su biya miliyan 4,899 yayin da ‘yan Arewa za su biya miliyan 4,699.

Har ila yau, maniyyata daga Yola da Maiduguri za su biya naira miliyan 4,679 a matsayin kudin aikin hajjin, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Kano: Kujerun Hajji 2,600 ne kacal aka sayar cikin 5,934

Yawan kujerun da aka ware a bana

Hukumar ta ware kujeru dubu 75 ga jihohin Najeriya 36 da kuma birnin Abuja inda ta ware kujeru dubu 20 ga kamfanoni masu zaman kansu da ke jigilar maniyyatan.

Daily Trust ta tattaro cewa a yau Litinin 12 ga watan Faburairu ce ranar karshe a hukumar ta saka dan biyan kudaden.

Duk da hukumar ba ta sanar da yawan wadanda suka biya kudaden ba, bincike ya tabbatar da cewa dukkan jihohin ba su cike ko da rabi na kujerun ba.

NAHCON ta sanar da kudin kujerar hajji

Kun ji cewa, Hukumar NAHCON ta sanar da kudin kujerar aikin hajjin bana bayan samun ragi a kudaden.

Hukumar ta ce maniyyata daga Kudancin Najeriya za su biya miliyan 4,899 yayin ‘yan Arewa za su biya miliyan 4,699.

Asali: Legit.ng

Online view pixel