Amfani 12 da aduwa ke yi a jikin dan adam

Amfani 12 da aduwa ke yi a jikin dan adam

- Itacen Aduwa sanannen abu ne a kasar Hausawa musamman a karkara

- Shi dai ‘ya’yan aduwa ana tsotsan sa ko kuma sha

- Man shi da ‘ya’yan shi ana amfani dasu wajen magunguna da dama

Itacen Aduwa itace ne dake fidda kwallaye masu matukar amfani a jikin mutum. Aduwa ta yi matukar suna a kasar Hausawa musamman a karkara.

Shi dai wannan ‘ya’yan aduwa tsotsansa akeyi ko kuma sha. Bayan sha da ake yi akan tatsi mai daga kwallan Aduwa. Ana kiranta da ‘Desert Date’ da turanci.

Bincike ya nuna cewa tsoson kwallon,man dake cikin ‘ya’yan, sannan kuma ita kan ta itacen na da matukar mahimmanci.

KU KARANTA: Miji ya yiwa matarshi wanka da tafasashen mai, saboda taki yarda ta koma gidanshi

Ga amfanin Aduwa a jikin mutum kamar haka:

1. Aduwa na kawar da cutar asma.

2. Mai fama da atini da zawo zai samu sauki idan ya tsotsi Aduwa

3. Aduwa na kawar da tsutsar ciki.

4. Yana maganin ciwon shawara.

5. Aduwa na maganin farfadiya.

6. Man kwallon Aduwa na rage kiba a jiki, idan ana girka abinci da shi.

7. Yana warkar da ciwo a jiki musamman idan ciwon ya zama gyambo.

8. Man Aduwa na maganin sanyin kashi da kuraje.

9. Yana kawar da kumburi.

10. Yana kawar da matsalar yin fitsari da jini.

11. Man Aduwa na gyara fatar mutum da hana saurin tsufa.

12. Yana kuma kawar da ciwon bugawan zuciya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng