Tsadar Rayuwa: ’Yan Kasuwa a Jihar Arewa Sun Koma Ga Allah Kan Halin da Ake Ciki, Bayanai Sun Fito

Tsadar Rayuwa: ’Yan Kasuwa a Jihar Arewa Sun Koma Ga Allah Kan Halin da Ake Ciki, Bayanai Sun Fito

  • Kungiyar ‘yan kasuwa a jihar Yobe ta koma ga Allah yayin da ake cikin wani irin yanayi na matsin tattalin arziki
  • Kungiyar mai suna UMAPO da ke jihar ta gudanar da salla ta musamman don neman taimako daga ubangiji
  • Shugaban kungiyar ya ce sun dauki matakin ne yayin da aka sake shiga matsin tattalin arziki tare da neman yafiyar ubangiji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe – Yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa a Najeriya, kungiyar ‘yan kasuwa ta koma ga Allah.

Kungiyar UMAPO da ke jihar Yobe ta gudanar da salla ta musamman don neman taimako daga ubangiji kan wannan tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni ga Tinubu: Ga hanyar shawo kan matsalar tsadar abinci da tattalin arziki

'Yan kasuwa sun koma ga Allah kan matsalar tsadar rayuwa
Yan Kasuwa a Jihar Yobe Sun Koma Ga Allah Kan Halin da Ake Ciki. Hoto: Bola Tinubu, Daily Trust.
Asali: Facebook

Mene shugaban kungiyar ke cewa?

Yayin da ya ke jawabi, shugaban kungiyar reshen birnin Potiskum, Alhaji Nasiru Mato ya ce sun yi sallar ce don neman taimakon ubangiji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mato ya ce sun dauki matakin ne yayin da aka sake shiga matsin tattalin arziki tare da neman yafiyar ubangiji, cewar Daily Trust.

A cewarsa:

“Matsin tattalin arziki da muka shiga da tsadar abinci duk sanadi ne na cire tallafin man fetur a kasar.
“Yan kasuwa na fuskantar kalubale da matsin tattalin arziki a wannan mawuyacin hali da ake ciki a Najeriya.”

Wace shawara ya bayar kan tsadar rayuwar?

Mato ya bukaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi har ma kananan hukumomi da su kafa kwamiti don dakile wannan matsalar.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke cikin wani irin yanayi na matsin tattalin arziki da kuma tsadar kayan abinci, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon APC ya gaji da tsarin Tinubu, ya nemi a sake zama kan tsare-tsaren gwamnati

Hakan nema ya saka Ministan Noma, Abubakar Kyari da cewa watakila su rufe iyakar Najeriya ganin yadda tsadar ke karuwa.

Kyari ya ce hakan zai dakile fitar da abincin da ake yi ba bisa ka’ida ba zuwa kasashe makwabtan Najeriya.

Sultan ya bukaci hukunta masu boye abinci

Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa kan tsadar rayuwa da ake ciki da ke addabar ‘yan Najeriya.

Sultan ya bukaci hukumar ICPC da ta dauki matakai kan masu boye kayan abinci har sai ya yi tsada su sayar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel