Ana Cikin Hali Matsi a Najeriya, Remi Tinubu Ta Fadi Lokacin da Sauki Zai Zo

Ana Cikin Hali Matsi a Najeriya, Remi Tinubu Ta Fadi Lokacin da Sauki Zai Zo

  • Oluremi Tinubu ta bayyana cewa canjin da ƴan Najeriya ke fatan samu zai ɗauki lokaci kaɗan, amma daɗi na nan tafe
  • Ta ba da wannan tabbacin ne a yayin da ake fama hauhawar farashin kayayyaki da kuma wahalhalun da manufofin Tinubu kan tattalin arziƙi suka jawo
  • Uwargidan shugaban ƙasan ta dage cewa da sabon shirin sabunta fata da kuma manufofin gwamnatin tarayya, matsalar za ta zama tarihi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara ƙamari, uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta tabbatarwa ƴan Najeriya cewa mawuyacin halin da suke ciki nan ba da daɗewa ba zai zo ƙarshe.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ta bayar da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ta yi da matan gwamnoni a fadar shugaban ƙasa a Abuja a ranar Litinin 5 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Uwar gidan Shugaba Tinubu ta yi ƙus-ƙus da matan gwamnoni a Aso Villa, bayanai sun fito

Remi Tinubu ta ba ƴan Najeriya tabbaci
Remi Tinubu ta gana da matan gwamnoni a Abuja Hoto: Sen. Oluremi Tinubu, CON
Asali: Facebook

Remi Tinubu ta ba ƴan Najeriya sabon tabbaci

Remi Tinubu ta ce shekarar 2024 shekara ce mai cike da zaman lafiya, ci gaba, wadata da nasarori ga al’ummar Najeriya baki ɗaya, inda ta ƙara da cewa ajandar sabunta fata ta Shugaba Tinubu na nan daram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uwargidan shugaban ƙasar ta yabawa matan gwamnonin bisa ƙoƙarinsu da goyon bayan da suka bayar a shekarar 2023, inda ta buƙacesu da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen magance buƙatun marasa galihu a jihohinsu, cewar rahoton Vanguard.

A kalamanta:

"Lokaci irin wannan yana buƙatar tunani mai zurfi, don haka, dole ne mu haɗa ƙarfinmu waje ɗaya. Bugu da ƙari, yanayin wahala na ɗan lokaci ne, ba da daɗewa ba zai shuɗe.
"Ofishina ne ke tafiyar da manufar shirin RHI don cika ajandar sabunta fata ta gwamnatin Shugaba Tinubu."

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan buƙatar magoya bayan gwamnan PDP da ake zargi da ta'addanci

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Caccaki Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan sukar manufofin Tinubu kan tattalin arziƙin ƙasar nan.

Bayo Onanuga, hadimin shugaban ƙasa Tinubu ya bayyana cewa Atiku har yanzu bai san inda aka dosa ba ballantana ya riƙa sukar manufofin gwamnatin Tinubu kan tattalin arziƙin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel