Rundunar ’Yan Sandan Najeriya Ta Fi Ko Ina Yawan Masu Garkuwa da Mutane, in Ji Seun Kuti

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya Ta Fi Ko Ina Yawan Masu Garkuwa da Mutane, in Ji Seun Kuti

  • Seun Kuti, dan marigayi Fela Kuti, shahararren mawakin nan na Najeriya ya zargi 'yan sanda da jagorantar kungiyoyin garkuwa da mutane
  • A cewar Seun Kuti, da yawa daga cikin masu garkuwa da mutane 'yan sanda ne da kansu, kuma suna karbar kudin fansa daga hannun jama'a
  • Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance matsalolin satar mutane a kasar, yana mai cewa akwai matsala a jami'an tsaron kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Shahararren mawakin nan na Najeriya Seun Kuti, ya yi kakkausar suka ga rundunar ‘yan sandan Najeriya, yayin da ya ke ba da labarin abin da ya faru a ofishin ‘yan sanda da ke Panti a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Kudin Fansa: Masu garkuwa suna barazanar hallaka mutanen Abuja 11 da aka sace

Da yake magana a wata tattaunawar kai tsaye a Instagram, Seun ya yi zargin cewa ‘yan sanda ne ke da hannu wajen satar mutane da ake yi a kasar, Leadership ta ruwaito.

Yan sandan Najeriya sun koma masu garkuwa da mutane
Yan sandan Najeriya yanzu sun rikide sun koma masu garkuwa da mutane - Seun Kuti. Hoto: @PoliceNG, @RealSeunKuti
Asali: Twitter

Yan sanda na karbar kudin fansa a hanun mutane - Seun

Da yake ba da labarin abin da ya faru a lokacin kama shi a shekarar 2023, ya ce an kulle shi tare da gungun masu laifi, ciki har da masu kisan kai da masu garkuwa da mutane, a cikin daki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi ikirarin cewa da yawa daga cikin masu yin garkuwa da mutane jami’an ‘yan sanda ne da kansu, wadanda ke aiki a matsayin jagororin kungiyar masu garkuwan.

Seun ya kuma yi ikirarin cewa 'yan sanda sun yi garkuwa da wasu 'yan Najeriya tare da tilasta musu biyan kudin fansa kamar yadda masu garkuwa da mutane ke bukata.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwamushe mutum 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Akwa Ibom

Seun Kuti ya roki gwamnati ta kawo karshen garkuwa da mutane

Ya kuma kwatanta neman belin da ‘yan sanda ke yi da karbar kudin fansa, yana mai jaddada cewa idan aka tilasta wa mutane su biya domin a sake su, to kamar hukuma ce ta yi garkuwa da su.

Ya kuma yi tsokaci kan lamarin Evans, wanda shi ne fitaccen mai garkuwa da mutane, inda ya nuna cewa duk da an daure shi, ba a rage yawan sace-sacen mutane ba.

Dan marigayi Fela Kuti, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta magance matsalolin satar mutane a kasar, yana mai jaddada cewa lamarin ya wuce tunanin mutane.

Zulum ya nada sabon Wazirin Borno

A wani labarin, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya nada sabon Wazirin Borno kamar yadda Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garba Al Amin El-Kanemi ya bukata.

Mutawali Bukar, mataimakin magatakardar jami'ar Borno ne aka nada matsayin sabon Wazirin Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel