Wasu matasan kabilar Tibi sun hallaka wani jami’in rundunar mayakan Sojan kasa a jihar Benuwe

Wasu matasan kabilar Tibi sun hallaka wani jami’in rundunar mayakan Sojan kasa a jihar Benuwe

A ranar Lahadi ne wasu matasan kabilar Tibi na jihar Benuwe suka sake kashe wani jami’in rundunar mayakan Sojan kasa a jihar Benuwe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Premium Times ta ruwaito matasan sun kashe jami’in Sojan ne yayin da yake tafiya tare da wani abokinsa akan babur da misalin karfe 2 na rana, inda suka shirya masa tarkon rago, kuma ya fada, a kauyen Gbeji dake cikin karamar hukumar Logo.

KU KARANTA: Iyayen yan matan Chibok sun mutu a wata mummunan hadarin Mota

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tuni aka mika gawarsa zuwa garin Makurdi, sai babu tabbacin asibitin koyarwa na jami’ar Makurdi aka kai shi, ko kuwa wani asibitin Sojoji ne dake garin Makurdi.

Wasu matasan kabilar Tibi sun hallaka wani jami’in rundunar mayakan Sojan kasa a jihar Benuwe
Sojan Najeriya

Sai dai wasu alkalumma da shelkwatar rundunar tsaro ta fitar ya nuna cewa marigayin shi ne jami’in Soja na goma sha biyar, 15, da aka kashe musu a jihar Benuwe, tun bayan barkewar rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Kimanin kwanaki uku da suka gabata ma an kashe wani jami’in Soja a karamar hukumar Gwer na jihar Benuwe, inda Sojoji suka mayar da mummunan martani ta hanyar kona gidaje da kashe kashe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng