Maza Gabanku: Dakarun Sojoji Sun Buɗe Wa Ƴan Bindiga Wuta, Sun Kashe Da Yawa a Jihar Arewa

Maza Gabanku: Dakarun Sojoji Sun Buɗe Wa Ƴan Bindiga Wuta, Sun Kashe Da Yawa a Jihar Arewa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga uku yayin da suka kai farmaki kauyen Chibi a jihar Taraba
  • Kwamandan rundunar Birged ta 6, Birgediya Janar Uwa ya yabawa dakarun sojin bisa wannan nasara, inda ya ce sun kwato makamai
  • Ya ce dakarun sojin ba za su yi ƙasa a guiwa ba har sai sun kawar da duk wani nau'in aikata laifuka a faɗin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga uku kuma sun samu nasarar kwato makamai da alburusai da ‘yan bindigar ke amfani da su a jihar Taraba.

Dakarun sojin sun samu wannan nasara ne a wani samame da suka kai ranar Alhamis a ƙauyen Chibi da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Shugaban tsaro, Christopher Musa.
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Uku, Sun Kwato Makamai A Jihar Taraba Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa rundunar sojin Birged ta 6 ce ta samu nasarar bayan tattara bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta'adda a yankin ƙauyen na Chibi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da cache guda 40 na harsashi na musamman 7.62MM daga hannun ‘yan bindigan.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamandan rundunar Birged ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya rabawa manema labarai.

Kwamandan ya kuma yabawa dakarun sojin bisa jajircewar da suka nuna wajen aiwatar da Operation din kuma aka samu nasara.

Yadda sojoji suka kashe yan bindiga a Taraba

Uwa ya jaddada aniyar sojoji na kawar da duk wani nau'in aikata laifuka a jihar Taraba tare da tabbatar da tsaro da jin dadin al'umma.

A rahoton Daily Trust, kwamandan sojojin ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun baƙunci lahira yayin da suka kai hari a jihar arewa, mutum 2 sun tsira

"A ranar Larabar da ta gabata ne sojoji suka samu gagarumar nasara ta kawar da wasu manyan ‘yan bindiga uku daga doron duniya.
“Haka zalika an samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, babur da barayin ke amfani da su, da fakiti guda 40 na harsashi na musamman.
"Lamarin ya afku a kauyen Chibi, inda dakarun 6 Brigade, yayin aiki da bayanan sirri, suka kai farmaki kan yan bindigan."

Sojoji sun jero abubuwan da suka jawo rikici a Mangu

A wani rahoton kuma Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana muhimman abu 2 da suka jawo tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Mangu, jihar Filato.

Kakakin hedkwatar tsaro, Janar Buba, ya ce kisan da wani makiyayi ya yi wa ɗan garin Mangu na cikin abubuwan da suka jawo rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel