Wasanni 5 na yara duk dan Najeriya ba zai manta
A kullum burin kowani karamin yaro shine ya girma ya manyan ta, sai dai kuma a irin halin rayuwan da muke ciki, manyan ma so suke su koma su zama yara, oh!
Lokaci zuwa lokaci zaka jama’a na tuna yarintan su, don su dan samu nishadi. Ga wasannin da yara suka fi so.
Tafa tafa
Ana yin wannan wasan ne ta hanyar mutum biyu ko sama da haka su dinga tafa hannayensu, ana yi ana waka, dadi.
Wasan rawa
Shi wannan wasan yara da yawa ake samu suna zagaye wani yaro a tsakiya, sai a dinga yi mai wake, shiko yana tika rawa.
Dara
Yara sun fi yin wannan wasan a kasar yarbawa, ana buga wannan wasan ne akan katako mai rami shida, sai a dinga daukan kwallon dabino ana sawa a cikin ramukan, kwallo hudu ake so a sa a kowane rami, a haka ake gane zakaran wasan.
Yar galagala
Zana layuka a kasa akeyi a wannan wasan, sai a raba su gida gida kamar gida 6 ko fiye da haka, yaro zai tsaya daga bakin layin farko ne, sai ya jefa karamin dutse cikin daya daga cikin gidajen, sai ya fara tsalle da kafa daya yana shiga kowani gida har ya kai gidan da dutsen shi ya fada, sai ya dauka abinsa, ya cigaba da tsalle har ya fita daga duka gidajen. Dokan wasan nan shine ba’a so dutsen ka ya dira akan layi, sai dai a cikin gida.
Ojiyo jiyo
Shi ko wannan wasan mutum biyu ko sama da haka ke yin sa, inda mutum daya zai dinga bin sauran yaran don neman kama daya daga cikin su, duk wanda ya kama daga nan shi zai cigaba da bin sauran yaran har ya kama wani, shima ya bi su, haka za’ayi tayi har a gaji.
Wani wasa kayi daga cikin wadannan wasanni?
Asali: Legit.ng