Kiwon Lafiya: Hanyoyi 6 na kara lafiya da gina Jiki

Kiwon Lafiya: Hanyoyi 6 na kara lafiya da gina Jiki

Lafiyar jiki abu ne da kowa ke bukata domin kuwa masana kiwon lafiya sun yi kididdiga akan cewa, da yawa daga cikin cututtukan dake kama jikin dan Adam su na bayuwa ne dangane da irin cimarsa.

Idan mutum ya kauracewa da yawa daga cikin nau'ukan abinci da ake sarrafasu a kamfanunnka, kama daga kifin gongoni zuwa lemuka na gongoni, to tabbas zai tsarkeke lafiyar jikinsa daga sunadaran calories.

Wannan sunadaran na calories su na da tasiri kwarai da gaske wajen karya garkuwar jikin dan Adam, domin kuwa su na jefa sassa daban-daban na jikin dan Adam cikin hadarin kamuwa da cututtuka.

Kiwon Lafiya: Hanyoyin kara lafiya da gina Jiki
Kiwon Lafiya: Hanyoyin kara lafiya da gina Jiki

Ga jerin hanyoyi 6 da za su kara habaka lafiya da gina jikin dan Adam

1. Yawaitar amfani da kayan hatsi irinsu; gero, dawa, acca, masara, uwa uba alkama, domin kuwa su na kara karfafa karfin jikin dan Adam da kuma bayar da kariyar cututtuka irinsu, ciwon zuciya, ciwon sukari da kuma ciwon daji.

2. Amfani da 'Ya'yan itatuwa da ganyayyaki:

3. Rage amfani da gishiri da kuma sarrafaffen sukari.

KARANTA KUMA: Kungiyar shugabannin musulmi na Najeriya ta mayar da martani akan kungiyar CAN

4. Ana bukatar mutum ya yawaita shan ruwa domin masana kiwon lafiya sun bayyana cewa ruwa ba ya taba yin yawa a jikin dan Adam saboda irin bukatuwar jiki ga ruwa.

5. Kauracewa barasa da sunadarin Caffeine, wannan sunadarin ana samun shi a cikin lemo na Coca Cola da kuma Naskofi

6. Rage amfani da nama da kwai na kajin gidan gona, domin kuwa sunadaran gina jikinsu ba daya yake da kajin hausa ba. Saboda haka ga mai bukatar sunadarin Protein a jikinsa, akwai irinsu gyada, gujjiya da kuma wake da suke kunshe da wannan sunadari.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng