Jami'an DSS Sun Hallaka Matashi Yayin Bin Layi a Gidan Mai? Hukuma Ta Yi Martani

Jami'an DSS Sun Hallaka Matashi Yayin Bin Layi a Gidan Mai? Hukuma Ta Yi Martani

  • Hukumar tsaro ta DSS ta musanta kisan wani matashi a Legas yayin turmutsu wurin bin layin gidan mai a yankin Obalande
  • Jami'an sun ce babu kamshin gaskiya kan labarin da ake yaɗawa kan kisan matashin inda ta bukaci a tuntubi 'yan sanda
  • Hakan ya biyo bayan hallaka matashin da wasu jami'an tsaro biyu suka yi bayan ya ƙi amincewa su shiga gabansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Hukumar DSS ta yi martani kan zargin jami'anta sun hallaka wani matashi yayin bin layin shan mai a jihar Legas.

Hukumar ta musanta cewa jami'anta ne suka hallaka matashin inda ta bukaci 'yan sanda su yi kwakkwaran bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Borno: Tubabbun 'yan Boko Haram sun sake daukar makamai, sun farmkaki jami'an tsaro

Hukumar DSS ta yi martani kan zargin kisan matashi a gidan mai
Jami'an DSS sun musanta zargon kisan matashi a gidan mai a Legas. Hoto: @OfficialDSSNG.
Asali: Twitter

DSS da musabbabin kisan matashin a Legas

Wannan ya biyo bayan kisan wani matashi a Legas yayin gumurzu bayan wahalar mai da ake fama da shi a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta DSS ta yi martanin ne a shafinta na X inda ta ke musanta cewa jami'anta sun yi ajalin matashin.

"Labarin cewa jami'an DSS biyu sun yi ajalin wani matashi a gidan mai a Obalande da ke Legas ba gaskiya ba ne."
"Ya kamata a tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a Legas domin samun karin bayani."

- Hukumar DSS

Martanin 'yan sanda kan kisan matashin

Daga bisani kakakin rundunar a Legas, Benjamin Hundeyin ya ce sun gano jami'in dan sanda da zargin aikata laifin.

Vanguard ta tabbatar da cewa Hundeyin ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 2 ga watan Mayu a Legas.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya bayan kama jarumin fina finai da zargin sace budurwa mai shekaru 14

"Wanda ake zargi da harbin an gano jami'in dan sanda ne da ke sashen Special Protection Unit a Lion Building da ke Legas."
"Tuni aka ƙaddamar da bincike domin gano gaskiya, sannan Kwamishinan 'yan sanda ya na ganawa da iyalan marigayin domin tabbatar da adalci a binciken."

- Benjamin Hundeyin

DSS sun bindige matashi a gidan mai

A wani labarin, ana zargin wasu jami'an DSS biyu sun yi ajalin wani matashi yayin bin layin shan mai a jihar Legas a ranar Laraba 1 ga watan Mayu.

Matashin mai suna Toheeb Eniasa ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ki amincewa jami'an sun shiga gabansa inda ya bukaci su bi layi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel