Maulidi: Atiku Ya Yi Martani Kan Harin Bam da Aka Yi Kan Bayin Allah a Kaduna, Ya Ba da Shawara

Maulidi: Atiku Ya Yi Martani Kan Harin Bam da Aka Yi Kan Bayin Allah a Kaduna, Ya Ba da Shawara

  • Yayin da ake cikin jimamin rashin 'yan uwa a Kaduna, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi martani
  • Atiku ya nuna alhinisa tare da tura sakon jaje ga iyalan wadanda su ka rasa ransu yayin harin inda ya yi musu addu'ar samun rahama
  • Ya kuma bukaci a yi binciken gaggawa don kare faruwar hakan a nan gaba da kuma bai wa wadanda su ka samu raunaka kulawa ta musamman

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Atiku ya bukaci ayi kwakkwaran bincike don tabbatar da zakulo wadanda su ka aikata wannan aika-aika.

Kara karanta wannan

A Dangi 1 kadai, Sojoji sun kashe mutane 34 da bama bamai wajen Maulidin Kaduna

Atiku ya yi martani game da harin bam Kan masu Maulidi a Kaduna
Atiku ya ba da shawarar taimaka wa wadanda su ka rasa ransu a harin bam a Kaduna. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Mene Atiku ke cewa game da harin bam kan masu Maulidi?

Dan takarar PDP ya bayyana haka a shafin X yayin da ya ke nuna alhini a yau Talata 5 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan jefa bam da rundunar sojin Najeriya ta yi kan masu Maulidi a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 3 ga watan Disamba yayin da kusan 80 su ka mutu da dama su ka samu raunuka, cewar TheCable.

Wane shawara Atiku ya bayar?

Yayin alhinin, Atiku ya ce:

"Na kadu da samun labarin mutuwar mutane da dama bayan an kai musu harin bam a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi.
"Abin takaici ne yadda wadanda su ka mutun su na bikin Maulidi a jihar, ya kamata a kiyaye irin wannan matsala yayin yaki da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Kisan masu maulidi a Kaduna: Dattawan Arewa sun magantu, sun ba gwamnati sharudda

"Ina kira ga jami'an tsaro da su yi bincike mai zurfi don kare faruwar hakan a nan gaba."

Atiku ya jajantawa wadanda su ka rasa rayukansu inda ya bukaci ba su kulawa ta musamman a asibitoci.

Har ila yau, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya shawarci bai wa iyalan wadanda su ka mutu taimako don rage musu radadin da su ke ciki.

Tinubu ya yi martani kan harin bam a Kaduna

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya yi martani game da harin bam da aka kai kan masu bikin Maulidi a jihar Kaduna.

Tinubu ya nuna alhinisa inda ya bukaci a yi binciken gaggawa don kare faruwar hakan a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel