Ku Kara Hakuri, Tinubu Na da Shirin Ciyar da Kasar Nan Gaba, Shawarin Minista Ga ’Yan Najeriya

Ku Kara Hakuri, Tinubu Na da Shirin Ciyar da Kasar Nan Gaba, Shawarin Minista Ga ’Yan Najeriya

  • An gudanar da taro, ministan shari’a ya ba da shawari kan wasu lamurran da suka shafi goben Najeriya a hannun Bola Tinubu
  • A cewar ministan, ya zama dole ‘yan Najeriya su yi hakiri batukar suna son ganin daidai a lamurran kasar baki dayanta
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da koka yadda mulkin Tinubu ke kokarin zame musu karfen kafa da jangwan saboda tsananin tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Ogun, jihar Kwara - Ministan shari’a a Najeriya, Lateef Fagbemi (SAN) ya bukaci ‘yan Najeriya da su goyi bayan ayyukan gyara kasa na Shugaba Bola Ahmad Tinubu, Punch ta ruwaito.

Ya kuma bayyana bukatar ‘yan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasa, inda yace ayyukan da ya dauko za su haifarwa Najeriya da da mai ido.

Kara karanta wannan

A mutunta shugabanni: Mufti Menk ya ba da shawarin yadda Najeriya za ta daukaka a duniya

Ku yi hakuri da Tinubu
A yi hakuri, Tinubu zai gyara kasa | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A kara hakuri kadan

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta bakin hadiminsa a fannin yada labarai, Kamarudeen Ogundele.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wani taron ahalinsa a garinsu Ijagbo a karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara, ya ce dole ne a yi hakuri don ganin daidai, rahoton Daily Post.

A cewarsa, ‘yan Najeriya da za su yi hakuri, shugaban kasa a shirye yake ya fitar da Najeriya da duhun da take ciki.

An fara ganin haske a tafiyar

Sanarwar ta ce:

“Shugaban kasa ba neman yabon kai yake ba. Yana neman hanyar gyara goben kasar ne.
“Ana rantsar dashi, ya bazama neman masu zuba hannun jari su shigo. Saboda haka, an fara ganin haske a tattaunawarsa da masu zuba hannu jaridaga kasashen waje.
“Abu daya da muke bukata shi ne a kara hakuri. Idan ka dasa bishiya, ba a rana daya take zuba ‘ya’ya ba."

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun kai samame maɓoyar yan bindiga a garuruwa 6, da yawa sun sheka lahira

A mutunta shugaba a ga daidai, Menk

A wani labarin, shahararren malamin addinin Musulunci, Mufti Ismail Musa Menk, ya ziyarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja.

Menk da tawagar masana na duniya sun ziyarci Tinubu ne a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, inda suka yi kira ga wanzar da zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Menk ya kara jaddada bukatar dukkan ‘yan Najeriya su zauna lafiya da juna tare da mutunta juna duk da bambancin addini da kabila domin ganin nasara a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel