An Bukaci Tinubu Ya Haramta Wa Wike Rike Mukami Har Abada Kan Abu Daya Tak, an Bayyana Dalili

An Bukaci Tinubu Ya Haramta Wa Wike Rike Mukami Har Abada Kan Abu Daya Tak, an Bayyana Dalili

  • Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam, Emeke Omeagbalasi ya bukaci Shugaba Tinubu da ya kori Minista Nyesom Wike daga mukaminsa
  • Emeke ya ce akwai zarge-zarge kan tsohon Gwamnan Ribas da jagorantar kisan gilla a shekarar 2020 a yankin Obigbo da aka zubar da jini
  • Omeagbalasi ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin 20 ga watan Nuwamba inda ya ce a haramta masa rike mukami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mai rajin kare hakkin dan Adam Kwamred Emeke Omeagbalasi ya bukaci a kori Minista Wike daga mukaminsa kan zagin ta'addanci.

Emeke wanda shi ne shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa ya bayyana haka a a yau Litinin 20 a watan Nuwamba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

An bukaci Shugaba Tinubu ya haramta wa Wike rike mukaman gwamnati
An bai wa Tinubu shawara kan korar Minista Wike. Hoto: Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Wike da aka nemi Tinubu ya kora?

Ya ce Wike na da alaka da wani ta'addanci da aka aiwatar a shekarar 2020 da aka aiwatar da kisan gilla a Obigbo, Independent ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar Emeke ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya kori Minsitan daga mukaminsa da kuma haramta masa rike duk wata kujera a kasar.

Kwamred din na zargin Wike ya hada baki da wasu mutane guda 12 wurin kisan gillar inda ya bukaci a haramta musu fita kasashen ketare.

Wane shawara aka bai wa Tinubu kan Wike?

Yace:

"Wike ya jagoranci mamaya da kuma yin amfani da karfi a ranar 21 a watan Oktoba na shekarar 2020.
"Ya gayyaci sojoji wadanda su ka kai mummunan hari kan 'yan kungiyar IPOB da ake zargi da hallaka sojoji shida da 'yan sanda hudu har ma da kona ofishin 'yan sanda."

Kara karanta wannan

An sake kama hatsabibin dilallin kwayoyi shekaru 7 bayan tserewarsa daga gidan yari a Abuja

Wannan na zuwa ne bayan korafe-korafe da al'ummar Musulmi su ka yi kan Wike da a sauya shi a mukamin Ministan Abuja a kwanakin baya.

Gumi ya bukaci Tinubu ya sauya Wike

Kun ji cewa, Sheikh Ahmed Gumi ya bukaci Shugaba Tinubu ya sauya Nyesom Wike a mukaminsa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Wike na shirin rusa wani bangare na masallacin Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel