An Garkame Babban Malamin Addini a Gidan Yari Kan Zargin Damfarar Miliyan 305, Bayanai Sun Fito

An Garkame Babban Malamin Addini a Gidan Yari Kan Zargin Damfarar Miliyan 305, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa an garkame wani fasto dan Najeriya mazaunin Birtaniya, Paul-Kayode Simon Joash, bisa zarginsa da aika laifin damfara
  • An tsare shi a gidan yari na Agodi, jihar Oyo, bisa zarginsa da damfarar akalla mutane Naira miliyan dari uku da biyar
  • An ba malamin kudaden ne da nufin samo takardun shaidar daukar nauyi ga mutanen da ke shirin zuwa Burtaniya don neman aikin yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ibadan, jihar Oyo - Rahotanni sun bayyana cewa an tsare wani fasto dan Najeriya mazaunin Birtaniya, Paul-Kayode Simon Joash, a gidan gyaran hali na Agodi, Ibadan, jihar Oyo.

Joash, wanda shi ne babban fasto na cocin The Great House Nation, an tsare shi a gidan yari na Agodi bisa zarginsa da damfarar akalla mutane uku Naira miliyan dari uku da biyar, jaridar The Nation ta ruwaito a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kama wani da kokon kan mutum sabon yanka a Ibadan, hotuna sun bayyana

Malamin majami'a, Joash
Duk da kasancewarsa malamin coci, ya damfari mutane uku sama da miliyan dari uku Hoto: Paul-Kayode Simon Joash
Asali: Facebook

An kunno wa fitaccen fasto, Simon Joash wuta

An bayar da rahoton cewa an ba shi kudaden ne da nufin samo takardun shaidar daukar nauyi ga wasu da ke shirin yin kaura zuwa Burtaniya don neman ayyuka da suka shafi kiwon lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce har tsawon shekara daya, ya gaza samar wa mutanen takardun.

An yi zargin, ya karbi Naira miliyan 134,823,750 daga mutum daya; Naira miliyan 30 mutum daya; Naira miliyan 135,177,750 daga mutum daya da kuma wani da ya karbi Naira miliyan 5,881,000 daga hannunsa, inda kudin gaba daya su ka tashi Naira miliyan 305,882,500.

Jami’an ‘yan sanda sun kama malamin a cocinsa biyo bayan korafin da aka ce wadanda abin ya shafa suka shigar a kansa.

Har ila yau, masu korafin sun yi ikirarin Fasto Joash yana satar kafa wajen shiga da fita daga Najeriya don kar ya hadu da su.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

Fasto ya damfari wata mata Naira miliyan 36

Wani malami mai suna Sule Shaibu, mai shekaru 70, da mataimakan shi, Wasiu Salami da Francis Akinola, sun gurfana gaban kotun majistare dake Iyaganku a Ibadan, a ranar Asabar, sakamakon zarginsu da ake da damfarar wata mata naira miliyan 36 don maganin aljanun da suka dameta.

Shaibu da mataimakanshi biyu na fuskantar zargi uku ne da suka hada da: hada kai wajen cuta, karbar kudi ta hanyar karya da damfara, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel