Tashin Hankali Yayin da Aka Kama Wani da Kokon Kan Mutum Sabon Yanka a Ibadan, Hotuna Sun Bayyana

Tashin Hankali Yayin da Aka Kama Wani da Kokon Kan Mutum Sabon Yanka a Ibadan, Hotuna Sun Bayyana

  • Rundunar yan sandan jihar Oyo ta gurfanar da wani da ake zargin matsafi ne, Hassan Kolawole a Ibadan
  • An tattaro cewa bai dade ba da aka kashe mutumin da aka samu kansa a hannun Kolawole domin dai sabon yanka ne
  • Yan Najeriya a soshiyal midiya sun shiga damuwa da samun labarin kisan gillar da aka yi wa mutumin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Rundunar yan sanda a jihar Oyo ta gurfanar da wani da ake zargin matsafi ne, Hassan Kolawole a ranar 10 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, an kama Kolawole mai shekaru 45 dauke da sabon kokon kan mutum a Ibadan, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

Yan sanda sun kama wani da kokon kai a Ibadan
Tashin Hankali Yayin da Aka Kama Wani da Kokon Kan Mutum Sabon Yanka a Ibadan, Hotuna Sun Bayyana Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An kama matsafi da kokon kan mutum a Ibadan

An gurfanar da wanda ake zargin a hedkwatar rundunar da ke Eleyele a karamar hukumar arewa maso yammacin Ibadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Blueprint ta rahoto, an kama Kolawole ne a karamar hukumar Ona Ara.

Bayan karin bayani daga rundunar yan sandar, masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu.

Legit Hausa ta tattaro wasu martani daga dandalin X a kasa:

@IamBlaccode ya ce:

"A hankali Ibadan ya fara zama mabuya da kogon matsafa. Ku tuna da batun Soka da wasu labarai masu alaka...Ya zama dole mutum ya dunga taka-tsan-tsan da ginin karkashin kasa da kangon gine-gine da ke dazuzzuka, a nan suke aiwatar da mugun nufinsu."

@The_khemist ya yi martani:

"Wayyo Allah na, wadannan kashe-kashe. Allah ka taimake mu."

@pacifik_cruise ya yi martani:

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa mutum 6 hukunci kan damfarar kakakin majalisa N38m

"Babu alamun nadama ko danasani a fuskarsa mai karfin nan."

Doris Michael ta rubuta:

"Wannan ya yi muni."

@Street_king_007 ya rubuta:

"Asirin Disamba ya yawaita kowa na so ya wataya."

An kama fasto da kokon kai

A wani labarin, mun ji cewa jami'an 'yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani Fasto mai suna Oyenekan Oluwaseyi da wasu mutane 3 kan mallakar kokon kai na dan Adam.

Legit ta tattaro cewa an tasa keyar wadanda ake zargin a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba zuwa ofishin 'yan sanda a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng