Yadda likitoci 12 ke barin Nigeria zuwa kasashen waje neman aiki kowanne mako

Yadda likitoci 12 ke barin Nigeria zuwa kasashen waje neman aiki kowanne mako

- Kungiyar likitocin cikin gida ta ce akalla abokan aikinsu 12 ne ke barin Nigeria kowanne mako zuwa kasashen wajen don neman aiki a can

- A kowanne watan Nuwamba, kungiyar na gudanar da wannan bukin bukin murnar zagayowar satin kiwon lafiya karkashin ARD-FCTA

- Kungiyar ta alakanta tabarbarewa fannin kiwon lafiya ga karancin albashi, rashin tsaro da kuma rashin fadada aikin likitanci a kasar

Kungiyar likitocin cikin gida ta ce akalla abokan aikinsu 12 ne ke barin Nigeria kowanne mako zuwa kasashen wajen don neman aiki a can.

Shugaban kungiyar likitocin cikin gida ta kasa reshen babban birnin tarayya Abuja, Michael Olarewaju, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Ya yi jawabin ne a lokacin da yake zayyanawa manema labarai ayyukan da aka tsara gudanarwa don bukin murnar zagayowar satin kiwon lafiya na 2018, wanda za ayi karkashin taken, "Tsiyayewar kwakwalwa: Kalubalen da gazawar fannin lafiya ke jawowa.'

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16

Yadda likitoci 12 ke barin Nigeria zuwa kasashen waje neman aiki kowanne mako
Yadda likitoci 12 ke barin Nigeria zuwa kasashen waje neman aiki kowanne mako
Asali: Depositphotos

A kowanne watan Nuwamba, kungiyar na gudanar da wannan bukin sati na kiwon lafiya karkashin ARD-FCTA, wanda mambobinsu ke gudanar da wasu ayyukan tallafin kiwon lafiya ga jama'a, da kuma kara karfafa dangantaka tsakaninsu da jama'ar da ke makwaftaka da su.

Mr Olarewaju ya ce kasa da likitoci 40,000 da suka yi rijista ne ke aikin likitanci a fadin kasar, mai dauke da mutane akalla 190m, wanda a cewarsa ya sanya da yawan 'yan Nigeria ba sa samun isasshen kiwon lafiya, sakamakon kashi 88 na likitoci a kasar ke zuwa wasu kasashe neman aiki.

Ya alakanta tabarbarewa fannin kiwon lafiya ga karancin albashi, rashin tsaro da kuma rashin fadada aikin likitanci a kasar.

Mr Olarewaju ya kuma yi nuni da cewa nauyin da ke tattare da likita daya ya kula da marasa lafiya da yawa na neman fin karfinsu, wanda wasu lokutan ke gajiyar da likitoci har su kasa baiwa marasa lafiya kyakkyawar kular da ya kamata akan lafiyarsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng