Tirkashi; Fasto ya damfari wata mata miliyan 36 akan cewa zai cire mata aljanu

Tirkashi; Fasto ya damfari wata mata miliyan 36 akan cewa zai cire mata aljanu

- Wani malami da hadiman shi biyu sun gurfana a gaban wata kotun majistare a kan zarginsu da ake da damfarar

- Shaibu mai shekaru 70 da mataimakan shi, Wasiu Salami da Francis Akinola sun damfari wata mata kudi har naira miliyan 36

- Alkalin kotun ya bada belinsu a kan naira miliyan hudu tare da tsayayyu guda biyu

Wani malami mai suna Sule Shaibu mai shekaru 70 da mataimakan shi, Wasiu Salami da Francis Akinola sun gurfana gaban kotun majistare dake Iyaganku a Ibadan a ranar Asabar sakamakon zarginsu da ake da damfarar wata mata naira miliyan 36 don maganin aljanun da suka dameta.

Shaibu da mataimakanshi biyu na fuskantar zargi uku ne da suka hada da: hada kai wajen cuta, karbar kudi ta hanyar karya da damfara.

Kamar yadda dan sanda mai gabatar da karar, Sajan Olalekan Adegbite, ya sanar, malamin da mataimakansa sun karba naira miliyan 36 daga wata mata mai suna Olayinka Ishioye da alkawarin shawo kan matsalarta.

Yace wadannan laifukan sun ci karo da sashi na 383 kuma abin hukuntawa ne a sashi na 390, sakin layi na 9, sashi na 419 da kuma sashi na 516 na dokokin jihar Oyo na 2000.

KU KARANTA: Matar Adam A Zango tayi maganar da ta firgita mutane kan rashin lafiyar Zee Pretty

Wadanda ake zargin sun musanta zarginsu da ake yi.

Alkali S.A. Adesina ya bada belin wadanda ake zargin a kan naira miliyan hudu tare da tsayayyu biyu.

Alkalin ya jaddada cewa tsayayyun dole su kasance 'yan uwan wadanda ake zargin kuma daya daga cikinsu ya kasance ma'aikacin gwamnati mai albashi mataki na 12. Ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu don cigaba da shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: