Dattawan Arewa Sun Tsoma Baki a Rigingimun Dauda/Matawalle da BUA/Dangote

Dattawan Arewa Sun Tsoma Baki a Rigingimun Dauda/Matawalle da BUA/Dangote

  • Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ba ta jin dadin sabanin da ya shiga tsakanin Dauda Lawal da Bello Muhammad Matawalle
  • Farfesa Ango Abdullahi wanda Shugaba ne a NEF ya fitar da jawabi inda yayi kira ga manyan da ke faman rikici su ajiye kayan yakinsu
  • Shugabannin NEF sun yi kira ga Alhaji Aliko Dangote da lhaji Abdussamad Isiyaku Rabiu su zama abin misali ga al’ummarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ganin yadda alaka ta yi tsami tsakanin wasu manya, kungiyar NEF ta Dattawan Arewacin Najeriya ta nuna takaici da rashin jin dadi.

A wani jawani da jagoran NEF, Farfesa Ango Abdullahi ya fitar a jiya, Leadership ta ce za a sasanta Aliko Dangote da Abdussamad Isiyaku Rabiu.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

Baya ga sabanin da aka samu tsakanin manyan ‘yan kasuwan na Afrika, kungiyar dattawan za ta kawo karshen rikicin siyasar jihar Zamfara.

Dattawan Arewa
Manyan Arewa za su yi wa Gwamnonin Zamfara sulhu Hoto: Dr Bello Matawalle/Dauda Lawal
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Ango ya nuna za su yi sulhu tsakanin Dauda Lawal da magabacinsa wanda yake karamin Ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle.

NEF ta ce a duba halin da Arewa ta ke ciki

Jawabin ya ce lura da halin da ake ciki a yau, NEF ta yi kira ga shugabannin da su ka samu sabani su yi hakuri, su duba maslahar yankin Arewa.

Vanguard ta rahoto Fafesan ya na cewa ya na da kyau shugabannin jihar Zamfara su nuna dattaku da sanin ya kamata domin a iya samun cigaba.

Jawabin Shugaban kungiyar Arewa

"Biyewa rikici na babu gaira-babu dalili zai karkatar da al’umma daga ainihin abubuwan da ke gabanta wajen neman kawo gyara.

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

Mutanen Zamfara su na fama da kalubale dabam-dabam, daga ciki akwai talauci, rashin tsaro da matsalar rashin karfin tattalin arziki.
A matsayin shugabanni, aikinmu ne magance wadannan matsaloli kuma mu samar da makoma mai kyau ga al’ummarmu.
Biyewa rigingimu, bata lokaci da dukiya ne da ya kamata ayi abubuwan da suka dace.

- Farfesa Ango Abdullahi

Kungiyar ta na so Alhaji Dangote da Abdussamad Rabiu su dukufa da kasuwancinsu, su zama abin misalin da zai amfani daukacin yankin Arewa.

Gwamnati ta ki kara kudin lantarki

A gefe guda, labari ya zo inda aka ji Gwamnatin tarayya ta fadi abin da ya sa ba za iya yi wa mutanen Najeriya karin kudin wutar lantarki ba tukun.

Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa har gobe gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin domin gudun farashin wuta ya nunku biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel