Zaben Gwamnan Kogi: Babban Malami Ya Hango Dan Takarar 'Mai Jama'a' Amma Ba Zai Yi 'Nasara' Ba

Zaben Gwamnan Kogi: Babban Malami Ya Hango Dan Takarar 'Mai Jama'a' Amma Ba Zai Yi 'Nasara' Ba

  • A yanzu dai, bai fi saura kasa da kwanaki biyar zaben gwamnan jihar Kogi ba; daya daga cikin zabuka uku da ake yinsu daban da na babban zaben kasar
  • Manyan jam'iyyun da ke takara a zaben sun hada da All Progressives Congress (APC), the Peoples Democratic Party (PDP), da kuma jam'iyyar Social Democratic Party (SDP)
  • Da ya ke jawabi gabanin zaben da aka zura idanuwa aga yadda zai gudana, malamin majami'a Godwin Ikuru, ya ce babu inda dan takarar SDP zai je a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lokoja, jihar Kogi - Ma'assasin majami'ar Jehova's Eye Salvation, manzo Godwin Ikuru, ya ce babu ta yadda za a yi dan takarar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka, ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi a zaben jihar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Barayi sun sacewa Najeriya man fiye da Naira Tiriliyan 4.3 a shekaru 5 Inji NEITI

Manzo Ikuru ya ce duk da Ajaka shi ne ya mafi shahara a cikin 'yan takarar, sai dai a cewar sa, "ba shi da taimakon na-sama".

Zaben jihar Kogi
Ajaka ba zai iya cin zaben gwamnan jihar Kogi ba, cewar Ikuru Hoto: Dino Melaye, Alhaji Ahmed Usman Ododo, Ademu Musa
Asali: Facebook

Kogi: "Murtala Ajaka ba zai ci zabe ba", Manzo Ikuru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin majami'ar ya yi hasashen cewa Ajaka zai yi makoma irin ta Peter Obi.

Jaridar Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Obi shi ne na uku a zaben shugaban kasa da ya gabata, wanda ya samu goyon bayan jama'a a zaben da aka gudanar cikin watan Fabreru.

Ikuru ya ce:

"Ita sa'a tana da muhimmanci, shi ya sa Allah ne kadai ke bayar da sa'a."
"Akwai wannan dan takarar, Ajaka. Yana da tarin masoya; mutane na binsa a zahiri. Amma ba shi da amincewar na-sama, kuma ba shi da sa'a. Amma mutane na binsa kamar yadda suka bi Peter Obi."

Kara karanta wannan

Ga mari, ga tsinka jaka: APC ta yi wa Peter Obi raddi kan batun shari’ar zaben 2023

"Ni ba fasto ba ne, ba kuma Bishop ba, sannan ni ba pope ba ne, kawai ni ma'aiki ne na ubangiji. Maganganun ubangiji ba na yara ba ne, na manya ne."
"Mutane suna ta tururuwa akan Muri Ajaka, amma zai ci zabe? Ba zai ci ba. Yana da nasibi a zahiri, amma ba shi da sa'a a badini."

Zaben Kogi: Ikuru ya fadi "dan takarar da Allah ya zaba"

A baya Legit Hausa ta ruwaito maku yadda Godwin Ikuru, ya ce Ahmed Ododo, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben jihar Kogi shi ne zabin Allah.

Da ya ke yin hasashen gabanin zaben da ke tafe, manzo Ikuru a cikin wani faifan bidiyo da ya sanya a Facebook ya bayyana cewa:

"Ina mika wannan sako mai karfi ga gwamnan jihar Kogi. Eh, zan kira shi gwamna domin shi ne Allah ya zaba. Eh, matashin da Yahaya Bello ya kawo, shi ne Allah ya zaba."

Kara karanta wannan

Sarkin Legas ya bai wa Tinubu, Atiku da Peter Obi muhimmin shawara bayan hukuncin kotun koli

"Don haka, mutanen Kogi, sun san abin da za su yi."

Melayeya fallasa kudirin Bello na yin tazarce karo na uku

Haka zalika, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Sanata Dino Melaye dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP ya yi zargin cewa Gwamna mai ci na jihar Kogi, Yahaya Bello, na kokarin ta zarce zango na uku a kan mulki ta hanyar kafa wakili.

Gwamna Bello, wanda ke a siradin karshe na zangon mulkinsa na biyu, yana goyon bayan ɗan takarar jam'iyyarsa ta APC, Usman Ododo, a zaben watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel