Zaben Kogi: Dino Melaye Ya Tona Asirin Gwamna Yahaya Bello Na Zarce Wa Zango Na Uku

Zaben Kogi: Dino Melaye Ya Tona Asirin Gwamna Yahaya Bello Na Zarce Wa Zango Na Uku

  • Sanata Dino Melaye ya bayyana ƙwarin guiwar cewa shi zai lashe zaɓe gwamnan jihar Kogi a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023
  • Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa ya ci zaɓe a shekarar 2019 duk da yana tsagin adawa a jihar da jam'iyyar APC ke mulki
  • Melaye ya ce Gwamna Yahaya Bello na amfani da Usman Ododo, ɗan takarar gwamna a inuwar APC domin ya ci gaba da mulki karo na uku

Jihar Kogi - Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, Dino Melaye, ya tona muhimmin abu game da Gwamna Yahaya Bello.

Sanata Dino Melaye, Ododo da Yahaya Bello.
Dino Melaye Ya Yi Ikirarin Gwamna Yahaya Bello Na Neman Ta Zarce Zango Na Uku Hoto: Dino Melaye, Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Melaye ya taƙali Gwamna Yahaya Bello gabanin zaɓe

Sanata Dino Melaye ya yi zargin cewa Gwamna mai ci na jihar Kogi, Yahaya Bello, na ƙoƙarin ta zarce zango na uku a kan mulki ta hanyar kafa wakili.

Kara karanta wannan

Da Gaske NWC Ya Kori Sakataren Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Daga Muƙaminsa? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna Bello, wanda ke a siraɗin ƙarshe na zangon mulkinsa na biyu, yana goyon bayan ɗan takarar jam'iyyarsa ta APC, Usman Ododo, a zaɓen watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma Sanata Melaye ya ce yana da yaƙinin cewa Yahaya Bello na shirye-shiryen ci gaba da mulki ne ta hannun Ododo.

A cikin shirin Siyasa a Yau na kafar talabijin na Channels da ya halarta ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, 2023, Sanata Melaye ya ce:

"Kar a yaudare ku cewa Yahaya Bello ba ya cikin takardar kaɗa kuri'a. A bayyane dai dodo ne a jiki amma Yahaya Bello ne ke neman wa'adi na uku ta hanyar wakili."
"Ba zan so wannan tattauna wa ta kasance a kan Yahaya Bello kaɗai ba, a'a zan so tallata jam'iyyata ta siyasa da kuma tallata abin da muka kudiri aniyar yi a jihar Kogi."

Kara karanta wannan

An Bayyana Ainihin Dalilin da Ya Sanya Wike Ya Gana da Bukola Saraki

Tsohon dan majalisar ya ce yana da kwarin guiwar kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC domin ta taba faruwa a baya a shekarar 2003 lokacin da PDP ta tsige Abubakar Audu.

Ya kuma yi takama da cin zaben sa na Sanata a karkashin jam’iyyar PDP duk da cewa Yahaya Bello ne gwamna a 2019, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.

Rigima Ta Ɓalle a APC a Majalisar Dattawa

A wani rahoton na daban Sanata Godswill Akpabi ya musanta zargin da aka masa cewa shi ya yi kutun Kotun Kotu ta tsige Sanata Elisha Abbo.

Hadimin shugaban majalisar dattawan ya ce babu dalilin da zai sa mai gidansa ya shirya wa abokin aikinsa bi ta da ƙulli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel