'Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Yari a Jihar Cross River, Sun Harbe Mai Gadi

'Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Yari a Jihar Cross River, Sun Harbe Mai Gadi

  • Wasu mahara da ake kyautata zaton mayaƙa ne sun kai sabon hari kan gidan gyaran hali a jihar Kuros Riba
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun bindige jami'i ɗaya har lahira sun kuma tafi da bindigarsa
  • Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar Kuros Riba ta tabbatar da kai harin amma ta ce za ta fitar da sanarwa nan gaba kaɗan

Jihar Cross River - Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai sabon hari gidan gyaran halin Afokang da ke jihar Kuros Riba.

Maharan waɗan da rahoto ya nuna cewa sun kutsa kai gidan gyaran halin daga wata hanyar shiga Kalaba da ke kusa, sun bindige jami'in tsaro mai gadin wurin.

An sake kai hari gidan gyaran hai a Najeriya.
Mai gadi ya mutu yayin da aka kai hari gidan yari Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Haka nan kuma 'yan bindigan sun ɗauki bindigar jami'in tsaron, sun yi awon gaba da ita, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gobara Ta Lakume Rayukan Mutane 2 a Gidan Mai Yayin Da Ake Tsaka da Tsadar Man Fetur, An Bayyana Dalili

A cewar wasu majiyoyi, mayakan ba su sami damar shiga harabar gidan yarin ba sai dai kawai sun aikata ta'asar su ne a babbar kofar shiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ce lamarin na iya kasancewa yana da alaka da ciyarwa saboda ana ta korafin cewa sabon kwanturola na jihar ya ƙaranta kayan abinci ga fursunoni.

Wane mataki hukumar gyaran hali ta ɗauka?

A halin yanzu, Kwanturolan ya kira taron gaggawa a babban ofishin hukumar da ke daura da filin shakatawa na Millennium, Kalaba, kan sabon harin gidan yarin.

Wani mazaunin yankin wanda ya bayyana sunansa da Godwin Esu, ya ce:

"Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare. Mun ji karar harbe-harbe, mun san daga gidan yari ya fito. Bayan wadanda suka yi harbe-harben sun tafi ne aka ce mana an kashe wani jami’i ɗaya.”

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen gyaran hali reshen jihar Cross River, DSC Effanga Etim, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Amma bai yi ƙarin haske kan abinda ya auku ba, a cewarsa nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa a hukumance, kamar yadda Ripples ta ruwaito.

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

Kuna da labarin A ranar 10 ga watan Oktoba, 2023, jihar Katsina ta buɗe wani sabonnbabi a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

A wannan shafi, za ku ji muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da sabuwar rundunar tsaron da ta ja hankalin ɗaukacin 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262