Yan Arewa da Ke Kasuwar Shanu a Jihar Abia Sun Koka Kan Wa’adin da Gwamnati Ta Ba Su Na Kwanaki 14

Yan Arewa da Ke Kasuwar Shanu a Jihar Abia Sun Koka Kan Wa’adin da Gwamnati Ta Ba Su Na Kwanaki 14

  • ‘Yan Arewa da ke kasuwar shanu a jihar Abia sun koka kan wa’adin kwanaki 14 da gwamnatin jihar ta ba su
  • Dilolin shanun a kasuwar Lobbanta da ke karamar hukumar Umunneochi sun roki Tinubu da Sarkin Musulmi da su kawo musu dauki
  • A martaninshi, Gwamnan jihar, Alex Otti ya bayyana labarin da kanzon kurege inda ya ce ba gaskiya ba ne

Jihar Abia – Shugabannin ‘yan Arewa da ke kasuwar shanu da ke karamar hukumar Umunneochi da ke jihar Abia sun roki Shugaba Tinubu da Sarkin Musulmi da su kawo musu dauki.

‘Yan kasuwar sun yi wannan rokon ne bayan gwamnatin jihar Abia ta ba su wa’adin kwanaki 14 da su tashi daga kasuwar, Dailt Trust ta tattaro.

'Yan kasuwar shanu da ke Abia sun koka kan wa'adin da gwamnati ta ba su
Gwamnatin Abia ta bai wa 'yan Arewa da ke Kasuwar shanu wa'adin kwanaki 14. Hoto: Bola Tinubu, Alex Otti.
Asali: Facebook

Wane korafi 'yan kasuwar ke yi a Abia?

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Tsaida Lokacin da Za a Fara Biyan Ma’aikatan N-Power Albashin Wata 9

Mataimakin shugaban dilolin shanun da ke kasuwar Lobbanta, Buba Abdullahi Kedemure ya ce su na korafin ne saboda wa’adin da gwamnatin ta ba su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kedemure ya jagoranci tawaga zuwa ofishin kungiyar National Concensus Movement a Kaduna don isar da korafin.

Ya ce sun kasance ma su bin doka inda su ke gudanar da kasuwancinsu tsawon shekaru ba tare da matsala ba amma yanzu an ba su wa’adi kan zargin boye ma su laifi a kasuwar.

Ya ce:

“Mu na rokon shugabanninmu da su saka baki wurin kira ga gwamnan da ya janye wannan wa’adin kwanaki 14 da ta ba mu.”

Wane martani gwamnatin Abia ta yi?

Shugaban kungiyar NCM, Dakta Auwal Abdullahi ya ce za su yi iya kokarinsu don ganin sun kare mutuncin ‘yan kasuwa daga Arewa a yankunan kabilar Ibo.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Sanda Suka Kama Fasto da Wasu Mutum 3 da Kokon Kan Dan Adam, Sun Fadi Abin da Za Su Yi da Shi

Ya tunatar da gwamnan Abia da sauran yankunan Kudu maso Gabas irin biliyoyin kasuwanci da kabilar Ibo ke da shi a Arewacin kasar ba tare da tsangwama ba, cewar Vanguard.

Yayin da yake martani, hadimin gwamnan Abia a harkar tsaro, MacDonald Ubah mai ritaya ya yi fatali da labarin inda ya ce jita-jita ce kawai babu gaskiya a ciki.

Ya gargdai wadanda su ka juya umarnin ta wata hanya da zai kawo sabani da tashin hankali don bata wa Gwamna Alex Otti suna.

Miyagu sun fille kan jigon LP a Abia

A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun fille kan jigon jam'iyyar Labour a jihar Abia.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun fille kan Maduka Zachary wanda shi ne daraktan kamfe a Uturu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel