'Yan Sanda Sun Kama Fasto da Wasu Mutane 3 da Kokon Kai A Jihar Ogun

'Yan Sanda Sun Kama Fasto da Wasu Mutane 3 da Kokon Kai A Jihar Ogun

  • 'Yan sanda sun cafke shugaban cocin Christ Liberty Evangelism, Fasto Oyenekan Oluwaseyi da kokon kan Adam
  • An kama Faston ne da wasu mutane uku wadanda tuni su ka amince da aikata laifin wurin yin tsafi don samun kudi
  • Rundunar ta ce bayanan da su ka samu daga jama'a ne ya ba su nasarar kama wadanda ake zargin a jihar Ogun

Jihar Ogun - Jami'an 'yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani Fasto mai suna Oyenekan Oluwaseyi da wasu mutane 3 kan mallakar kokon kai na dan Adam.

Legit ta tattaro cewa an tasa keyar wadanda ake zargin a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba zuwa ofishin 'yan sanda a jihar.

Jami'an 'yan sanda sun cafke Fasto da kokon kan dan Adam
'Yan Sanda Sun Kama Fasto da Kokon Kayi a Ogun. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Da su wa aka kama Faston da kokon kan dan Adam?

Sauran wadanda aka kaman sun hada da Ibrahim Agbowewe mai shekaru 30 da Suleiman Ogunbunmi mai shekaru 40 sai Gafari Akinsanya mai shekaru 57.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Shugaban 'yan sanda zai tafi turai taron da zai sauya lamarin tsaron Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun shirya yin amfani da kokon kayunan ne don yin tsafi, cewar Punch.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jama'a ne su ka taimaka da bayanan sirri bayan zargin wasu al'amura a kewayen, Ladunliadinews ta tattaro.

Bayan samun rahoton, rundunar ta yi gaggawar isa wurin tare da kama su bayan samunsu da motar kirar Toyota da rago da kuma katuwar kwarya.

Wane martani 'yan sanda su ka yi kan kama Faston?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Omotola Odutola ta tabbatar da kamen mutane hudu inda ta ce dukkansu sun amince da laifinsu.

Ta ce:

"Mun kama mutane hudu wadanda tuni sun tabbatar da aikata laifin da su ke shirin yi na amfani da kayan wurin yin tsafi na kudi.

Kara karanta wannan

Mummunan hadari ya jefa ahalin mutane 3 a makoki, da yawa sun jikkata a jihar Legas

"Yanzu haka ana kan bincike don bankado bayanai wanda za a yi amfani da su a gaba."

'Yan sanda sun kama mata da cin zarafin mijinta

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Ribas ta cafke matar aure da ta watsa wa mijinta tafasasshen man gyada a jihar.

Matar mai suna Hope Nwala ta aikata hakan ne bayan samun 'yar hatsaniya da mijin nata mai suna Nwanko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel