Kamfanin Sukarin Dangote Na Daukar Ma'aikata Fiye da Dubu 7 Ko Wace Shekara

Kamfanin Sukarin Dangote Na Daukar Ma'aikata Fiye da Dubu 7 Ko Wace Shekara

  • Kamfani Aliko Dangote da ke samar da sukari a Najeriya ya bayyana irin kokarin rage matsalar ayyukan yi da ya ke a kasar
  • Kamfanin ya ce ya na daukar dubban ma'aikata aiki inda ya ce a ko wace shekara ya na daukar fiye da mutane dubu 7
  • Babban manajan ayyuka a kamfanin, Bello Dan Musa shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Numan

Jihar Adamawa - Kamfanin Dangote na sukari da ke Numan a jihar Adamawa na daukar ma'aikata dubu 7 duk shekara.

Bello Dan Musa, babban manajan ayyuka a kamfanin shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Numan, Legit ta tattaro.

Kamfanin Dangote na daukar ma'aikata dubu 7 ko wace shekara
Kamfani Sukari Na Dangote Na Daukar Ma'aikata Ko Wace Shekara. Hoto: Dangote Group.
Asali: Facebook

Meye kamfanin Dangote ke cewa kan aikin yi?

Dan Musa ya ce dubban mutane ne ke aiki kai tsaye a kamfanin yayin da fiye da dubu 7 ake dauka yayin da ake sarrafa kayayyaki a kamfanin.

Kara karanta wannan

Gaza: Saudiyya Ta Kira Taron Musulmai, Fafaroma Ya Tsawata Wa Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yanzu kamfanin sukari na Numan na fitar da Tan 4,800 a rana wanda zai karu zuwa Tan 6,000 a karshen 2023, Newspeak ta tattaro.

Har ila yau, zai iya karuwa zuwa tan 9,800 a karshen 2024 da kuma tan 15,000 a gaba.

Ya ce:

"Kamfanin Dangote na sukari da ke Numan shi ne kamfani mafi samar da yawan sukari a Najeriya."

Legit ta ji ta bakin wasu kan sanarwar kamfanin Dangote:

Isa mai Faci ya ce

"Idan har haka ne to lallai za a rage zaman banza a kasar kuma zai tallafa wa matasa ma su zaman banza."

Sani Muazu ya ce idan da tun kafa kamfanin ake haka ai da tuni rashin aikin yi ya ragu a kasar da kaso mai yawa.

Yusuf Abubakar ya ce:

"Matsalar da ake samu aikin kamfanin ma ya dawo sai wanda ka sani, ya kamata a bude ko wa ya cika tsakani da Allah."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Nemi Cin Sabon Bashin Dala Miliyan 400 Daga Bankin Duniya

Wane ci gaba ake samu a kamfanin na Dangote?

Mamallakin kamfanin, Alhaji Aliko Dangote ya ce bayan kammala ayyukan kamfanin, za su iya samar da ayyukan yi fiye da dubu 300 kai tsaye da kuma wadanda ba kai tsaye ba.

Hakan zai kara rage masu zaman banza a kasar wanda kuma zai inganta tattalin arzikin Najeriya.

Yayin ganawa da 'yan jaridu, babban daraktan kamfanin, Chinayya Judex ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a kamfanin dalilin karuwar sarrafa kaya a kamfanin.

Dangote ya yi martani kan rage farashin siminti

A wani labarin, kamfanin Dangote ya yi martani kan jita-jitar cewa ya rage farashin siminti a kamfanin.

Dangote ya karyata labarin da cewa ba shi da tushe kuma babu kamshin gaskiya a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel