Abubuwa 5 da suka fi jan hankalin mata a tattare da namiji

Abubuwa 5 da suka fi jan hankalin mata a tattare da namiji

Mata suna da banbanci hakazalika maza. Babu wani abu da ake amfani dashi wajen gwajin namiji mai nagarta. Wasu na duba irin ingantacciyar rayuwa ne inda wasu kuwa suna kallon rayuwa mai cike wadata. Amma wasu matan da yawa sun amince da wadannan halayen ko abubuwan da suke matukar son a tattare da namiji.

1. Sanya annashuwa

Duk mutumin da zai sa mace cikin annashuwa zai iya janye hankalinta tare da dasa soyayyarsa a zuciyarta. Kowa na da bukatar abokin zama mai saka shi cikin farin ciki koda kuwa ana cikin halin jarabawa.

2. Saukin kai da kula

Ba sai mutum ya tseratar da mutane yayin gobara bane za a kira shi da mai saukin kai a cikin jama'a ba. Namiji mai saukin kai da kula na iya sanya mace ta fada son shi ba kadan ba. A lokutan da damuwa ta samu mace, tana bukatar namiji mai kula a tare da ita.

3. Gaskiya

Babu mai son makaryaci. Gaskiya kuwa babbar nagarta ce a tattare da namiji. Namiji mai gaskiya shine wanda zai iya sanar dake gaskiyar lamari ba tare da cin amana ba. Gaskiya da biyayya a hade suka.

DUBA WANNAN: Imo: Korarren gwamna PDP ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a karo na farko

4. Soyayyar gaskiya

Namiji mai iya nuna wa mace soyayya a koyaushe yana iya tafiya da zuciyarta. Akwai hanyoyin bayyana soyayya masu tarin yawa. Budewa mace kofar gida ko ta mota, rike mata hannu yayin tsallake titi ko kuna shawagi. Kananan abubuwa ne dai ke bayyana tsantsar soyayya.

5. Nuna wa mace ita ta musamman ce

Mata da yawa na son namiji ya nuna musu sun kasance na musamman. Yabawa mace kwalliya, girki ko wani kokari da tayi don birgeka na kara mata soyayyar namiji. Duk namijin da ke nuna wa mace ita ta dabance na samun matsuguni mai girma a zuciyarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel