Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Shawarwari Ganin $1 ta Zarce N1000

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Shawarwari Ganin $1 ta Zarce N1000

  • Hukumar IMF ta yabi cire tallafin man fetur da karya darajar Naira da gwamnati da bankin CBN su ka yi a Najeriya
  • Shugabannin IMF sun bada shawarar a kara ruwa, idan aka yi amfani da wannan shawara, karbar bashi zai kara wahala
  • Yanzu Dala ta yi mahaukacin tashi a kasuwar canji, watanni kadan da daidaita farashi da bankin CBN ya yi kokarin yi

Morocco - Hukumar IMF mai bada lamuni a duniya ta yi kira ga Babban bankin Najeriya watau CBN ya cigaba da kara ruwa kan bashin kudi.

A rahoton Daily Trust, jagora a IMF, Daniel Leigh ya na ganin cewa karin ruwan ne zai taimaka wajen rage tsadar kaya da ake fuskanta a yau.

A yayin da ya ke jawabi wajen gabatar da rahoton bankin duniya a garin Marakesh a Moroko, Daniel Leigh ya ba bankin CBN wannan shawara.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

Bola Tinubu
Dala ta lula a mulkin Bola Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

IMF ta yabi manufofin Bola Tinubu

IMF ta gamsu da yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur da daidaita kudin kasashen waje bayan ya karbi mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta nuna matakan da Bola Tinubu ya dauka za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.

Abebe Aemro Selassie ya bada shawarar ayi hattara da tsarin farashin kudin waje, ya bada shawara ga gwamnatin kasar ta tallafawa marasa karfi.

Wasu masana su na ganin karin darajar ruwa ba za ta saukake lamari ba kamar yadda ake tunani, a karshe sai dai hakan ya durkusa kasuwanci.

Dalar Amurka ta kai N1025 a BDC

Punch ta ce ‘yan kasuwa sun fara wayyo Allah ganin yadda Naira ta karye a kan Dala, yanzu ana saida $1 ne tsakanin 1, 005 zuwa 1, 030.

Ku na da labari tun da bankin CBN ya bar ‘yan kasuwa su tsaida darajar Naira, dalar kasar Amurka ta ke hawan sukuwa a kan kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

"Bola Tinubu ya yi kuskure" - 'Dan canji

A karshen makon jiya wani ‘dan canji da ke kasuwanci a garin Zariya ya fada mana su na sayen Dala a kan N980, yanzu farashin ya sauka kasa.

Da ya ke magana da Legit, ‘dan kasuwan ya koka da gwamnatin Bola Tinubu, ya ce sun fi jin dadin sana’arsu a lokacin Muhammadu Buhari.

A cewarsa kuskuren da aka yi shi ne barin darajar Naira da aka yi ta rika lilo.

Solomon Dalung a kan takardun Tinubu

An ji labarin yadda Solomon Dalung wanda tsohon Ministan wasanni da matasa ne ya fito da takardunsa domin ya nuna ya je makarantar boko.

Dalung ya ce zargin da ake yi wa BolaTinubu ya jawo abin magana sosai, a duk abin da ke faruwa, ya ce laifin hadiman shugaban kasa ne kurum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel