Ministan Buhari Ya Fito da Takardun Karatunsa, Ya Fadi Masu Jawowa Tinubu Cikas

Ministan Buhari Ya Fito da Takardun Karatunsa, Ya Fadi Masu Jawowa Tinubu Cikas

  • Barista Solomon Dalung ya tofa albarkacin bakinsa a kan zargin da wasu su ke yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Tsohon Ministan wasanni da matasan ya ce tuhumar da ake yi wa shugaban kasa ta jawowa mutanen Najeriya zargi
  • Dalung ya tabbatarwa duniya ya yi karatun digiri a jami’a, ya kalubalanci masu ja da hakan su nemi hujja daga UNIJOS

Abuja - Tsohon Minista a gwamnatin tarayya, Solomon Dalung, ya zargi hadiman shugaban kasar Najeriya da rashin yin abin da ya kamata.

A game da lamarin takardun karatun Mai girma Bola Ahmed Tinubu, Solomon Dalung ya fadawa tashar Channels TV akwai laifin hadimai.

Atiku Abubakar ya na zargin Bola Tinubu a kotu da yin karya a kan satifiket din da ya gabatarwa hukumar INEC domin shiga takara a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Abin Da Ya Sa Tinubu Ya Yi Wuf Ya Nada Sababbin Mukamai 5

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu Hoto: @nosasemota
Asali: Twitter

Dalung ya ga laifin hadiman Tinubu

Da aka yi hira da ‘dan siyasar a makon nan, sai ya ce masu ba shugaban kasa shawara su na damalmala lamarin a maimakon wanke shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta ce Dalung ya yi bayanin hikimar fito da takardunsa domin duniya ta gani, ya ce zargin wannan badakala ya bata sunan kasar.

Abin da Solomon Dalung ya fada

"Shugaban kasar Najeriya da mukarrabansa na siyasa su na zuwa daga wannan kotu zuwa wannan a Amurka da Najeriya a kan takardun.
Abin da ya ke faruwa yanzu ya jawo ana zargin duk wanda ya ke da satifiket a Najeriya.
Su na magana, su na kara tsokano abubuwan da mutane za su fake da su domin kara nauyi a kan shugaban kasar.
Na fito da takarduna a fili. Duk wanda bai gamsu ba, zai iya matsawa jami’ar Jos su fito da sakamakon jarrabawa na."

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu Ya Jawowa Mahaifinsa Suka Saboda Yawo a Jirgin Shugaban Kasa

- Solomon Dalung

Shugaban kasa Tinubu ya zama abin tausayi

The Cable ta rahoto tsohon jagoran na APC mai-ci ya ce ya na ganin darajar shugaban kasa, bai murna da abubuwan da ke faruwa da shi.

A hirar da aka yi da shi, Dalung ya yi ikirarin zargin da ake yi wa Bola Tinubu ta shafi kowa, amma ya tabbatar da cewa bai neman ci masa mutunci.

Badakalar takardun Tinubu

Basheer Lado ya ce su na sane da zargi maras tushe da yake kewaye da Shugaban kasa, Sanatan ya ce lamarin ya jawo surutu a fadin Najeriya.

Kamar yadda rahoto ya zo Sanatan ya na mai fatan kotun koli za ta wanke Bola Tinubu, wannan ya nuna ba ya goyon bayan Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel