HEDA dsr sun bukaci Shugaban kasa ya wargaza kwamitin Salami, ya dawo da Magu

HEDA dsr sun bukaci Shugaban kasa ya wargaza kwamitin Salami, ya dawo da Magu

- HEDA da wasu Kungiyoyi su na so a dakatar da binciken Ibrahim Magu

- Kungiyoyin su na ganin kwamitin Ayo Salami ba zai iya yin adalci ba

- A ra’ayin wadannan kungiyoyi, binciken na iya kai wa ga abin kunya

Kungiyoyin Human Environmental Development Agenda da wasunta sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da binciken Ibrahim Magu.

Wadannan kungiyoyi sun bukaci Muhammadu Buhari ta yi fatali da kwamitin Ayo Salami da aka kafa domin ya binciki zargin da ke wuyan Mista Ibrahim Magu.

Kungiyar wajen a takardar da ta aika wa shugaban kasar, ta ce zai yi wuya ayi wa Magu adalci.

KU KARANTA: Malami ne ya hana a taso da keyar Diezani ta dawo Najeriya ba ni ba - Magu

The Cable da Premium Times sun rahoto cewa shugabannin HEDA, da kungiyoyin Global witness, Cornerhouse, da Re: Common sun sa hannu a wannan takarda.

Kungiyoyin nan su ka ce an dauki lokaci mai tsawo da sunan ana binciken tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC ba tare da an gano gaskiyar komai ba.

A dalilin wannan, kungiyoyin su ka nemi gwamnatin Buhari ta wargaza kwamitin Ayo Salami domin Najeriya ta guji yin abin kunya a gida da gaban Duniya.

A cewar kungiyoyin, ba su adawa da binciken hukumar EFCC, sai dai tsoronsu shi ne, tun farko an nuna kwamitin ba zai yi gaskiya a wajen wannan bincike ba.

KU KARANTA: Magu ya yi jawabin farko bayan ya fito

HEDA ta bukaci Shugaban kasa ya wargaza kwamitin Salami, ya dawo da Magu
Ibrahim Magu Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Ya kamata Buhari ya san ana yi wa binciken da ake yi wa Magu kallon aikin banza ne kawai da yunkurin cin zarafin tsohon shugaban hukumar inji kungiyoyin.

Su ka ce kwanaki fiye da 120 kenan kwamitin da aka ba kwana 45 ya na aiki, amma babu abin da ya fito.

A makon da ya gabata kun ji cewa ana jita-jitar Donald Trump zai jarraba sa’arsa a 2024. Trump zai koma harin kujerar Shugaban kasa a wani zaben mai zuwa.

Na-kusa da Trump su na ba shi shawarar ya tsira da girmansa ya yi harin gaba bayan ya fadi zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel