Gini Bene Mai Hawa 4 Ya Rufto Kan Mutane, Ana Fargaban Ya Rutsa Da Gommai

Gini Bene Mai Hawa 4 Ya Rufto Kan Mutane, Ana Fargaban Ya Rutsa Da Gommai

  • Kuma dai, wani ginin bene ya sake ruftawa da mutane da dama a kudu maso kudancin Najeriya
  • Ana fargaban mutane da dama na cikin gidan da ginin benen ya fadawa a birnin jihar Akwa Ibom
  • .Ruftawan gine-gine a Najeriya ya zama ruwan dare a kwanakin baya-bayan nan

Uyo - Wani ginin bene mai hawa hudu a titin Imam Street Uyo, babbar birnin jihar Akwa Ibo ya rufta da mutanen da ba'a san adadinsu ba har yanzu.

An tattaro cewa wannan gini ya rufto kan wani ginin daban misalin karfe 6:30 na yammacin Asabar.

Kodinetan hukumar bada agaji na gaggawa NEMA na yankin kudu, Mr Godwin Tepikor, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, cewar DailyTrust.

Yace kawo yanzu an tsamo mutane hudu daga cikin ginin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Ginin
Gini Bene Mai Hawa 4 Ya Rufto Kan Mutane, Ana Fargaban Ya Rutsa Da Gommai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Wani gini mai hawa hudu bayan Bankin Zenith dake Akah Road by Plaza, Uyo, Akwa Ibom ya rufta kan wani gini. An ganin akwai mutane cikin ginin na kasa."
"An kaddamar da yunkurin ceto mutane kuma an tsamo mutum 4 kawo yanzu. Ku saurari karin bayani."

.Ruftawan gine-gine a Najeriya ya zama ruwan dare a kwanakin baya-bayan nan.

Cikin makonni uku da suka gabata, gidahen sun rufta a Abuja, Legas, Kano, Oyo da Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel