Jerin Mutane 11 Da Tinubu Zai Karrama Su A Ranar Bikin 'Yancin Najeriya

Jerin Mutane 11 Da Tinubu Zai Karrama Su A Ranar Bikin 'Yancin Najeriya

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu zai karrama 'yan Najeriya 11 da lambar yabo yayin da ake shirin bikin samun 'yanci a kasar.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wannan na daga cikin hobbasar Hukumar Wayar da Kan Jama'a (NOA) ta yi don cusawa mutane kishin kasa.

Jerin wadanda Tinubu zai karrama 11 a ranar 'yanci
Cikakken Sunayen Mutane 11 Da Tinubu Zai Karrama. Hoto: Bola Tinubu, NTA News.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu zai karrama mutanen?

Daraktan hukumar, Dakta Garba Abari shi ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Tarayya, Abuja.

Ya ce Tinubu zai ba da lambar yabon ne a ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit ta tattaro muku wadanda za su samu lambar yabon:

1. Marigayi Taiwo Michael Akinkunmi - shi ne wanda ya tsara tutar Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

2. Marigayi Salaudeen Akano - Sojan da ya tsayar da tutar Najeriya da tsakar dare yayin bikin 'yanci a 1960.

3. Marigayi Onwurah Chiazor Zonyanuno - kwamandan Salaudeen da ya tsayar da tutar Najeriya a 1960.

4. P. O Aderibigbe - ya ba da gudunmawa wurin wakar taken Najeriya.

5. Marigayi Benedict Odiase - shi ya gudanar da kidan 'yan sanda, The Nation ta tattaro.

6. Marigayiya Felicia Adebola Adedoyin - ita ta kirkiri taken Najeriya na biyu.

7. Adewuri - kawar Adedoyin da ta gabatar da ita ga shugaban kasa.

8. John A. Ilechukwu

9. Eme Etim Akpan

10. B.A. Ogunnaike

11. Sota Omoigui

Mutane 11 za a karrama su ne saboda gudummawar da su ka bayar ta bangarori da dama a kasar yayin da wasun su ke raye.

Najeriya ta samu 'yancin kai a hannun Turawan kasar Ingila a shekarar 1960 a ranar 1 ga watan Oktoba bayan gwagwarmaya da wasu daga cikin shugabannin kasar su ka yi.

Kara karanta wannan

Eid-el-Maulud: Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Alhamis a Matsayin Ranar Hutu

Kasashen Nahiyar Afirka da dama kafin samun 'yancin kansu, sun kasance karkashin mulkin Turawa na kasashe daban-daban a duniya da su ka mulkesu.

Jerin ministocin Tinubu ma su karancin shekaru

A wani labarin, bayan nadin ministoci da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi, an samu ma su karancin shekaru a cikinsu.

An yabawa Shugaba Tinubu kan irin wannan namijin kokari da ya yi wurin bai wa ma su karancin shekaru dama irin wannan ta mukamin minista.

Legit Hausa ta jero muku sunayen ministocin guda bakwai da ke tsakanin shekaru 30 zuwa 40.

Asali: Legit.ng

Online view pixel