Hannatu Musawa, Shu’aibu Audu, Da Sauran Ministocin Shugaba Tinubu Masu Karancin Shekaru

Hannatu Musawa, Shu’aibu Audu, Da Sauran Ministocin Shugaba Tinubu Masu Karancin Shekaru

An yaba ma shugaban kasa Bola Tinubu kan shigar da sabbin shugabanni da matasa a majalisarsa yayin da ya nada matasa da mata da dama a matsayin ministoci.

Idan aka yi lissafi, akalla ministoci bakwai ne ke a ganiyar shekaru talatin da farkon arba'in.

Tinubu ya nada mata da matasa a majalisarsa
Hannatu Musawa, Shu’aibu Audu, Da Sauran Ministocin Shugaba Tinubu Masu Karancin Shekaru Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ga jerinsu a kasa:

1. Betta Edu

Shugaban kasa Tinubu ya nada likitar mai shekaru 37 kuma yar siyasa a matsayin ministar harkokin jin kai da yaki da talauci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ita ce mafi karancin shekaru a cikin ministocin sannan ita ce minista mace ta farko daga jihar Cross River.

2. Olubunmi Tunji-Ojo

Kamar yadda shafinsa na Wikipedia ya nuna, an haifi dan siyasan na jihar Ondo a ranar 1 ga watan Mayun 1982. Shugaban kasa Tinubu ya nada shi a matsayin ministan harkokin cikin gida.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

Kafin nadin nasa, an zabe shi domin ya wakilci mutanen mazabar Akoko ta arewa maso gabas/Akoko ta arewa maso yamma na jihar Oyo a majalisar wakilai tsakanin 2019 da 2023.

3. Imaan Sulaiman-Ibrahim

An haife ta a ranar 19 ga watan Afrilun 1980, kuma ta shahara a bangaren kasuwanci da siyasa kafin Shugaban kasa Tinubu ya nada ta mukami.

An nada yar siyasar haifaffiyar jihar Nasarawa a matsayin karamar minista harkokin yan sanda mace ta farko, kuma an yaba nadin nata a matsayin wacce ta cancanta.

4. Hannatu Musawa

An bayyana ta a matsayin daya daga cikin ministocin shugaban kasa Tinubu mafi karancin shekaru, wacce ke da kwarewar aiki iri-iri a Najeriya da Ingila. Ita ce ministar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira ta yanzu.

Musawa ta taba aiki a matsayin mataimakinyar kakaki kuma mataimakin daraktan harkokin kamfen na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC. Ana rade-radin shekarunta 43.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Lauya ya tafi kotu, ya nemi a garkame wasu ministocin Tinubu bisa dalili 1

5. Shuaibu Audu

Shugaban kasa Tinubu ya nada Audu, ma’aikacin banki kuma dan siyasa wanda aka haifa a ranar 6 ga watan Nuwamba, 1980, a matsayin ministan bunkasa karafa.

Dan marigayi Abubakar Audu, gwamnan farar hula na farko a jihar Kogi, wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 1992 zuwa 1993, ya tsaya takarar neman tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamna mai zuwa a jihar Kogi amma ya sha kaye a hannun Ahmed Ododo.

6. Joseph Utsev

Shekarun ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli 43 kuma ana yi masa kallon daya daga cikin shugabannin siyasar Najeriya masu tasowa.

Utsev ya kasance malami, dan siyasa, dan jin kai, dan kasuwa kuma mai gudanarwa wanda ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Muhalli a Jihar Benue.

7. Doris Uzoka-Anite

Shugaban kasa Tinubu ya nada matashiyar yar siyasar jihar Imo wacce aka haifa a ranar 16 ga watan Oktoban 1981 a matsayin ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samo Sabon Bashi Na Dala Miliyan 700 Daga Bankin Duniya, Cikakken Bayani

Ta kasance likita kuma kwararriya a fannin hada-hadar kudi wacce ta yi aiki a matsayin kwamishinar kudi da hada-hadar tattalin arziki a jihar Imo.

Gaskiya ta bayyana game da wani bidiyo da ke ikirarin Hannatu Musawa tana busar hayaki

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo da aka wallafa a dandalin X wanda aka fi sani da Twitter da Facebook ya nuno wata mata tana busa hayaki da rawa a wajen wani taro.

An yi ikirarin cewa matar da ke bidiyon ministar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira, Hannatu Musawa ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel