Gaskiya Ta Bayyana Game Da Wani Bidiyo Da Ke Ikirarin Hannatu Musawa Tana Busar Hayaki

Gaskiya Ta Bayyana Game Da Wani Bidiyo Da Ke Ikirarin Hannatu Musawa Tana Busar Hayaki

  • Ministar al'adu, Hannatu Musawa, ta sake jan hankali bayan wani bidiyo da ya yadu ya nuno wata mata tana rawa da busa hayaki
  • Masu amfani da soshiyal midiya da ke yadfa bidiyon sun yi zargin cewa matar Musawa ce, lamarin da ya janyo mata suka
  • Wani dandalin binciken kwakwaf ya yi ikirarin cewa ba Musawa bace a cikin bidiyon

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wani bidiyo da aka wallafa a dandalin X wanda aka fi sani da Twitter da Facebook ya nuno wata mata tana busa hayaki da rawa a wajen wani taro.

An yi ikirarin cewa matar da ke bidiyon ministar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira, Hannatu Musawa ce

Ba gaskiya bane bidiyon Hannatu Musawa tana busar hayaki
An Yi Bidiyon Ministar Tinubu, Hannatu Masawa Tana Busa Hayaki Da Rawa? Gaskiya Ta Bayyana Hoto:Hannatu Musa Musawa
Asali: Facebook

Rahoton karya game da Musawa tana busa hayaki a wajen shagali

Legit Hausa ta gano ikirarin a Facebook da dandalin X.

Kara karanta wannan

“Rabona Da Wanka Shekara 1”: Yar Najeriya Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo, Tana Neman Agaji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani rubutu da aka yi ya ce:

"Ministar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira ta Tinubu, Hannatu Musawa tana bikin murnar nadinta a wani wuri a Najeriya. #Dubi daya daga cikin ministar mu tana zukar hayaki a bainar jama'a, abin kunya ne ga yan Najeriya a matsayin kasa."

Amma da gaske matar da ke rawa a bidiyon Musawa? Dandalin binciken gaskiya, Africa Check ya yi bincike.

Bayan bincike, shafin yanar gizon ya ce matar da ke cikin bidiyon ta taka rawa ne ga wata wakar yarbawa.

Amma Musawa Bafulatar usuli ce kuma yar jihar Katsina.

Harshen yarbanci da aka rera wakar da shi a bidiyon, ba yare ne da ake yi a tsakanin yan arewa ba da har Musawa za ta fahimce shi da kuma taka rawarsa.

Dandalin ya kuma ce ya duba hotunan Musawa da dama sannan ya kwatanta shi da na matar da ke cikin bidiyon -"ba mutum daya bane".

Kara karanta wannan

Yadda Likita Ya Yanke Jiki Ya Mutu Bayan Ya Shafe Tsawon Awanni 72 Yana Aiki a Asibitin LUTH

Akwai wani dan banbanci a suffar fuskarsu, kala da kuma yanayin shigarsu, dandalin binciken ya bayyana.

Hannatu Musawa: Shin masu yi wa kasa hidima na iya zama minista? Falana, sauran lauyoyi sunyi martani

A wani labarin, manyan lauyoyi a Najeriya na cigaba da tafka muhawara kan sahihancin nada Hannatu Musawa, wadda bata kammala bautar kasa ba, a matsayin ministar bunkasa al'adu da shugaba Tinubu yayi.

Yayin da wasu lauyoyin ke cewa hakan bai sabawa doka ba, wasu basu amince ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel