Murna Ta Koma Ciki Yayin da Gobara Ta Hallaka Mutane 100 Ana Tsaka da Shagalin Bikin Daurin Aure

Murna Ta Koma Ciki Yayin da Gobara Ta Hallaka Mutane 100 Ana Tsaka da Shagalin Bikin Daurin Aure

  • Wata mummunar gobara da ta tashi a wani wurin daurin aure a Al-Hamdaniya da ke lardin Nineveh na Arewacin Iraki ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 100 tare da jikkata wasu 150 na daban
  • Mummunan lamarin ya faru ne a yayin da daruruwan mutane ke ta murnar bikin, yanzu haka ana ci gaba da binciken musabbabin tashin gobarar
  • A halin da ake ciki kuma, rahotanni sun nuna cewa kayan kwalliyar wurin bikin na daga cikin abin da ya kara ta’azzara karuwar gobarar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Nineveh, Iraki - Sama da mutane 100 ne aka samu rahoton sun mutu yayin da wasu 150 suka jikkata sakamakon tashin gobara a wani bikin aure a gundumar Hamdaniya da ke lardin Nineveh na kasar Iraki.

BBC Pidgin ta ruwaito cewa daruruwan mutane ne ke hallara a wurin daurin auren a Qaraqosh da ke Arewacin lardin Nineveh na kasar Iraki lokacin da wata gobara ta kama wurin da yammacin ranar Talata 26 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Gobara ta kashe ango da amarya da mutane 100
Yadda gobara ta kashe ma'aurata da baki 100 | Hoto: BBC Pidgin
Asali: Facebook

A halin yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba amma rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne bayan an kunna wuta a wurin bikin.

Bayanai daga gwamnan jihar

Da yake martani kan lamarin, mataimakin gwamnan Nineveh, Hassan al-Allaq, ya shaidawa Reuters cewa mutane 113 ne aka tabbatar da mutuwarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, kafar labaran Iraki ta INA ta ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu ya kai akalla 100, yayin da wasu 150 suka jikkata.

Sai dai, duk da haka gwamnan ya ce ba a kayyade adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata ba saboda yadda yawan ke karuwa.

Gobara ta cinye amarya da ango

An ce sabbin ma’auratan na daga cikin mutanen da suka mutu, kamar yadda hukumar lafiya ta kasar ta tabbatar.

A halin da ake ciki dai jami'an tsaro na ci gaba da neman gawarwakin mutanen da suka kone da kuma wadanda suka tsira da rayukansu da ma wadanda suka jikkata.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

Hakazalika, hukumomin kasar na ci gaba da bincike don gano tushen wutar don kare aukuwar irin haka a nan gaba.

Kana naka Allah na nashi

A wani labarin na daban, wasu ahali sun shiga babban jimami yayin da mutum tara suka bakunci kiyama a hatsarin mota gabanin biki.

An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a jihar Bayelsa, inda aka ce mahaifi da mahaifiyar ango na daga cikin wadanda suka mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel