Allah Sarki: Wani Ango ya mutu wajen bikinsa a Jihar Ebonyi

Allah Sarki: Wani Ango ya mutu wajen bikinsa a Jihar Ebonyi

Wani bala’i ya aukowa mutanen Kauyen Amasiri da ke cikin karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi, inda wani Ango mai suna Mista Chukwuemeka Onwuka ya fadi a wajen bikinsa.

Kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto, Chukwuemeka Onwuka ya kife ne a lokacind ake cikin walimar bikin aurensa da Onyinyechi Amadi Ugbor. Nan take aka sheka da shi zuwa asibiti.

Bayan zuwa wani asibiti ne, Angon ya cika kafin ya isa hannun Likitoci. Wannan Ango Likitan idanu ne a asibitin Garin Bende a jihar Abia. Amaryar kuma ta fito ne daga Kauyen Amadi Ugbor.

Kamar yadda wadanda abin ya faru a gabansu, su ka bayyana, sun ce wannan Ango ya tika rawa tare da ‘Yan uwa da Aboka arziki a wajen walimar da aka shirya domin murnar daurin aurensa.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin taimakawa Mawaka da Makadan Afrika

“Bayan an yi rawa ne sai aka sanar da cewa wani ya batar da agogonsa a taron. Da aka ji cewa babu wanda ya zo ya nemi cigiyar wannan agogo, sai aka nemi a koma wani zagayen rawan."

Wannan mai bada labarin abin da ya auku ya cigaba da cewa: “A lokacin da Angon ya yi yunkurin zuwa gaban jama’a ya fara rawa kenan, sai ya fadi kasa, ya fara fitar wani kumfa daga bakinsa.”

“Nan-take mutane su ka yi maza su ka dauke shi, aka fara yi masa fifita, amma aka ga babu wani alamun samun sauki. Daga nan ne aka yanke shawarar a ruga da shi zuwa wani asibiti." Inji sa.

Bayan an sheka da Angon zuwa asibitin da ke kusa ne sai Likita ya nemi a garzaya da shi wani babban asibiti mai suna Mater Hospital da ke Garin Afikpo. Kafin a isa asibitin, Angon ya rasu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel